Ranar 7 ga wannan watan ne dai za a fara Gasar Kwallon Kafa ta Duniya ta 'yan kasa da shekara 17 a kasar India.
Kasasahe hudu ce ke wakiltar Afirka ta Yamma a gasar - wato Ghana da Guinea da Mali da kuma Nijar, wadda karon farko ke nan da za ta shiga wata gasar kwallon kafar duniya da hukumar FIFA ta shirya.
Kwallon kafa, wasa ne mai matukar farin jini ga matasan Afirka, inda za ka ga 'yan shekara daban-daban na buga tamola a duk inda suka samu fili cikin unguwa.
Yayin da ake tunkarar gasar 'yan kasa da shekara 17, mu kuma za mu kawo muku rahotanni na musammam kan kwallon kafar matasa, inda a yau Mohammed Abdu ya je wani filin kwallo a Kano don ganin yadda matasan ke sa zuciyarsu a kwallon kafa.
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Matasa Ke Wasan 'Yar Tile A Kano
Description : Ranar 7 ga wannan watan ne dai za a fara Gasar Kwallon Kafa ta Duniya ta 'yan kasa da shekara 17 a kasar India. Kasasahe hudu ce ke wak...
Rating :
5