Mai gabatar da shaidun kara Orji Chukwuma, ya shaida wa Babbar Kotun Ikoyi da ke Lagos yadda hadimin Jonathan mai suna Waripamo-Owei Dudafa ya taya Patience Jonathan jidar tsabar kudi har naira bilyan 5.1.
Ya bayyana haka ne a gaban Mai Shari’a Mohammed Idris. An gurfanar da Dudafa ne tare da wani mai suna Joseph Iwuejo, wani tsohon jam’in kula da harkokin kudi, wanda ake tuhuma da laifin taimaka masa wajen jidar kudin.
Mai gabatar da kara ya kara nuna irin harkallar Dudafa da Iwuejo a fili a gaban kotu, inda ya gabatar da hujjojin cewa sun yi amfani da sunayen Taiwo Ebenezer da Olugbenga Isaiah.
An ce tsakanin Yuni 2013 da Yuni 2015 sun jidi makudan kudaden da su ka kai adadin naira bilyan 5.1.
Chukwuma, jami’in binceke na ofishin EFCC, ya ci gaba da shaida wa kotu cewa akwai wani dan canji mai suna Murtala Abubakar, wanda ya amsa cewa ya sha amsar bilyoyin daloli sau da sama daga hannun su Dudafa.
“Sai mu ka gano cewa Chukuma ya ba Abubakar sunayen asusun bankunan da zai rika tura kuden bayan ya canja su.” Inji Chukwuma, jami’in EFCC.
Chukwuma ya kara shaida wa kotu cewa har cikin fadar shugaban kasa Dudafa ke shiga Patience Jonathan na loda masa kudi ya na jida.
Kamar yadda mai baincike ya kara yin bayani, ya ce Dudafa ya rika yin amfani da sunan wasu kamfanoni na bogi da kuma na gare, irin su ‘ABY Resources Limited, Avalon Global Property Development Limited, Pluto Property da Investment Company Limited’ da kuma sunayen wasu gidajen cin abinci na zamani da su ka hada da Delakes Fast Food and Restaurant da sauran su.
Sai da ishi kuma Dudafa, ya yi roko da yawun lauyansa cewa kotu ta ba shi fasfo din sa, domin ya samu ya fita kasar waje neman magani.
Shi kuwa mai gabatar da kara, Mista Oyedepo, ya roki kotu kada a bari Dudafa ya fice zuwa kasar waje, domin a ta bakin sa, EFCC ta rubuta wa asibintin gwamnatin jihar Lagos cewa su duba Dudafa domin su bayyana irin rashin lafiyar da ya ce ta ke damun sa, da nufin sanin ko za a iya yi masa magani a nan Najeriya.
Mai gabatar da kara ya ce har yanzu ya na jiran ba’asi daga asibitin.
Ganin haka, sai alkali ya daga shari’ar zuwa ranar 24 Ga Oktoba domin a tattauna yiwuwa ko rashin yiwuwar amincewa da rokon da ya yi. Sannan kuma ranakun 14 da 15 Ga Nuwamba, 2017 a ci gaba da shari’a
Source: Premium Hausa
Title :
Yadda Hadiman Jonathan Suka Taya Patience Satan Biliyan 5.1
Description : Mai gabatar da shaidun kara Orji Chukwuma, ya shaida wa Babbar Kotun Ikoyi da ke Lagos yadda hadimin Jonathan mai suna Waripamo-Owei Dudafa ...
Rating :
5