Jami'an kula da dabbobin daji sun kama wata damisa bayan kusan sa'a 36 da aka gano tana cikin wani kamfanin kera motoci.
Masu ceto sun samu damar yi mata allurar kashe jiki, bayan da aka dauki tsawon lokaci ana nemanta a kamfanin Maruti Suzuki da ke garin Manesar, wanda ba shi da nisa da birnin Delhi.
An fara gano damisar ne da sanyin safiyar Alhamis a kamarar bidiyo ta CCTV, daga bisani kuma kamarar ta ci gaba da nunota.
Masu aikin dare sun fice gaba daya daga cikin ginin, aka kuma rufe kamfanin gaba daya.
Kamfanin motocin na Maruti Suzuki shi ne mafi girma a Indiya, inda ake kera kusan motoci miliyan daya ko wacce shekara.
A lokacin da dubban ma'aikatan da ke aikin safe suka isa, dole ta sa aka tsayar da su a waje har sai da ma'aikatan gandun daji 12 da kimanin 'yan sanda 50 suka isa kamfanin don neman damisar da kuma fitar da ita.
Masu aikin ceton sun kai awaki biyu da danyen nama don jawo hankalin damisar ta fito daga inda ta buya
An gano damisar ne a kamarar CCTV a sashen injina, wanda ke da girman ekta shida.
Wani dan jarida a yankin ya shaida wa BBC cewa masu aikin ceton sun kai awaki biyu da danyen nama don jawo hankalin damisar ta fito daga inda ta buya.
Wani jami'in gandun daji Vinod Kumar, ya shaida wani kamfanin yada labarai cewa wasu mutanen kuma sun yi ta jefa abubuwa masu tartsatsin wuta don firgita damisar.
Amma daga baya an gano damisar aka kuma yi mata allurar kashe jiki, sannan hukumomi suka tabbatar wa da BBC cewa babu sauran fargaba.
Wani babban jami'in kula da gandun daji na Indiya R Anand, ya shaida wa BBC cewa, "Tuni aka kai damisar asibiti don tabbatar da lafiyarta kuma za a mayar da ita daji daga baya.
A Indiya dai ana yawan samun rikice-rikice tsakanin mutane da dabbobin daji, inda dabbobi kamar giwaye da damisa ke yawan shiga gari.
Akwai a kalla damisa 12,000 zuwa 14,000 a Indiya, inda kuma aka kiyasta cewa ana kashe daya a duk rana.
A bara ma wata damisa ta shiga wata makaranta a garin Bangalore har ta ji wa mutum shida rauni, wadanda suka yi kokarin kama ta.
An shafe sa'a 10 kafin a samu damar cafke damisar a kuma yi mata allurar kashe jiki.
Sai dai duk da haka ta sake tserewa daga inda aka ajiye ta bayan mako guda.
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Damisa Tasa Aka Rufe Kamfanin Motoci A India
Description : Jami'an kula da dabbobin daji sun kama wata damisa bayan kusan sa'a 36 da aka gano tana cikin wani kamfanin kera motoci. Masu ceto...
Rating :
5