Sa'o'i 24 gabanin Maryam Abdullahi ta kammala karatun aikin likita ne harin bam mafi muni a tarihin kasar Somaliya ya yi ajalinta.
Maryam tana daya daga cikin daruruwan mutanen da harin da aka kai birnin Mogadishu ya rutsa da su ranar Asabar.
'Yar uwar marigayiyar, Anfa'a, ta shaida wa BBC cewa lamarin ya kidimata "kwarai da gaske".
"Danginmu sun girgiza sosai, musamman mahaifinmu wanda ya taho Mogadishi daga birnin Landan domin ya halarci bikin yayeta, amman maimakon hakan sai ya halarci jana'izarta."
Anfa'a ta ce ta yi magana da 'yar uwarta minti 20 kafin tashin bam din da ya jawo mummunar asarar rayuka da dukiya a Mogadishu.
"A wanna lokacin tana cikin asibitin Banadir Hospital inda take aiki. Ta gaya min tana jiran wasu fayel-fayel daga asibiti." Daga nan sai ta dauki alkawarin da Ubangiji bai ba ta ikon ciwa ba, "zan kira ki zuwa an jima," in ji marigayiyar.
Wani wakilin Sashen Somali na BBC a wajen da lamarin ya auku ya ce Otel din Safari ya rufta kuma mutane da dama sun makale a barazugan ginin.
Wani shaida da ke zaune a birnin, Muhidin Ali, ya shaida wa AFP cewa ita ce "fashewa mafi girma da na taba gani, ta daidaita wajen gaba daya".
Hakazalika, daraktan asibitin Madina Hospital, Mohamed Yusuf Hassan, ya ce matakin harin ya tayar mishi hankali.
"Abin da ya faru jiya ya wuce hankali, ban taba ganin irin wannan ba, mutane da dama sun rasa rayukansu, gawarwaki sun kone kurmus."
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Bam Yakashe Yarinya Ana Gobe Zata Zama Likita
Description : Sa'o'i 24 gabanin Maryam Abdullahi ta kammala karatun aikin likita ne harin bam mafi muni a tarihin kasar Somaliya ya yi ajalinta. ...
Rating :
5