A ranar Litinin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta bayyana wanda zai lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da babu kamarsa a shekarar 2017.
'Yan takarar sun hada da dan wasan Real Madrid da Portugal Cristiano Ronaldo da dan Argentina mai wasa a Barcelona Lionel Messi da kuma Neymar dan Brazil mai buga tamaula a Paris St-Germain (PSG).
Wannan ne karo biyu da hukumar za ta gudanar da bikin bayan da ta raba gari da mujallar Faransa wacce take gudanar da kyautar Ballon d'Or.
Ga bayanan kokarin da 'yan wasan suka yi a 2017
CRISTIANO RONALDO (Real Madrid da Portugal)
Kungiya - wasa 36, ya ci kwallo 33
Tawagar Portugal - wasa 11, ya ci kwallo 11
Kofin da ya ci: Guda 3 - LaLiga da Champions League da Spanish Super Cup
LIONEL MESSI (Barcelona da Argentina)
Kungiya - wasa 45, ya ci kwallo 46
Tawagar Argentina - wasa 6, ya ci kwallo 4
Kofin da ya ci: Guda daya - Copa del Rey
NEYMAR (Barcelona da PSG da Brazil)
Kungiya - wasa 38, kwallaye 23
Tawagar Brazil - wasa 6, kwallo 2
Kofin da ya ci: Guda daya 1 - Copa del Rey
Source: BBC Hausa
Title :
Waye Zai Lashe Gwarzon Dan Kwallon Bana A Cikin Neymar,Ronaldo Ko Messi
Description : A ranar Litinin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta bayyana wanda zai lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da babu kamarsa a shek...
Rating :
5