Koci Jose Mourinho ya ce ba ya jin cewar a Manchester United zai kawo karshen aikinsa na horar da tamaula.
Mourinho mai shekara 54, wanda ke shekara ta biyu a yarjejeniyar da ya kulla da United, bai taba yin kaka hudu ba a kungiyoyi bakwai da ya jagoranta.
A lokacin da ake hira da shi a wani gidan talabijin a Faransa, Mourinho ya ce Paris St-Germain kungiya ce mai kyau.
Ya kara da cewa, ''Ni koci ne mai buri da son yin wani abun sabo''.
Mourinho, wanda tsohon kocin Chelsea da Real Madrid da Inter Milan da kuma Porto ne, ya shaida wa TF1 Telefoot cewar ba ya jin zai yi ritaya a Manchester United.
Kocin, wanda ya ci League Cup da kofin Zakarun Turai na Europa a farkon kakar da ya jagoranci United, ya ce akwai wani abu na musamman a Faransa, kamar inganci da matasa.
Source: BBC Hausa
Title :
Watakila Mourinho Yakoma Faransa Da Kocin
Description : Koci Jose Mourinho ya ce ba ya jin cewar a Manchester United zai kawo karshen aikinsa na horar da tamaula. Mourinho mai shekara 54, wanda k...
Rating :
5