Kotun dake unguwar Ebute Meta jihar Legas ta gurfanar da wata mata, Ngozi Obasi, mai shekaru 31 da ta kama da laifin kokarin kashe mijinta, Igwe Obasi, ta hanyar zuba tafashasshen ruwan barkonu a gaban sa.
‘Yar sandar da ta shigar da karan Kehinde Omisakin ta cewa Ngozi ta aikata hakan ranar 1 ga watan Oktoba da misalin karfe uku na asuba a cikin gidansu dake titin Fatiregun St.Ilaye a Ebute Meta bayan wata ‘yar gaddaman da ta auku tsakaninsu.
Wanda ta shigar da kara ta ce aikata irin hakan ya saba wa doka ta 230 na kundin tsarin mulkin jihar da ya shafi aikata irin wadannan laifuffuka. Duk da cewa kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa aikata irin wannan laifin kan sa a daure mutum a kurkuku har sai gawa.
Alkain kotun Tajudeen Elias ya bada belin matar akan Naira 100,000 tare da shaidar takardan biyan haraji ga gwanatin jihar Legas na tsawon shekaru uku sannan ya daga da sauraron karan zuwa 16 ga watan Oktoba.
Source: Premium Hausa
Title :
Wata Mata Ta Watsa Wa Mijinta Tafasasshen Ruwan Borkono A Gabansa
Description : Kotun dake unguwar Ebute Meta jihar Legas ta gurfanar da wata mata, Ngozi Obasi, mai shekaru 31 da ta kama da laifin kokarin kashe mijinta, ...
Rating :
5