Wasikun da ke cike da bakin ciki daga Barack Obama a lokacin da yake matashi zuwa budurwarshi sun nuna rayuwar wani mai shekara 20 da ke fama da rashin tabbas na launin fata da matsayi da kuma kudi.
Matashi Mista Obama da Alexandra Mcnear, wanda Obama ya hadu da shi a California, ne suka rubuta wasikun.
Wasu daga cikinsu sun nuna kalubalen da shugaban Amurka na gaba ya fuskanta daga farko a lokacin yana aikin da ba ya kauna domin kawai a ci gaba da rayuwa.
A kwanan nan ne aka wallafa wasikun a dakin karatu na Rose da ke jami'ar Emory ta saya a shekarar 2014.
"An rubuta wasikun da kyau kuma sun bayyana ba'asi da wani matashi ke yi na neman sani da kuma neman sanin asalinsa," in ji daraktan dakin karatun.
"Sun nuna irin abubuwan da dalibanmu suka fi damuwa da su- kuma dalibai a ko ina suke fuskanta."
Tazara mai tsawo
An rubuta wasikun ne tsakanin shekarar 1982 zuwa 1984, shekara biyar kafin Mista Obama ya fara zuwa zance gun matar da ya aura daga baya, wato Michelle.
A daya daga cikin wasikun na farko-farko, ya rubuta cewa: "Ina da yakinin cewa kin sani na kewarki, kuma na damu da ke matuka, yardar da na yi da ke ta kai zurfin teku, kuma soyayyata (gareki) na da yawa."
An karkare wasikar ne : "Masoyinki ne, Barack."
Amman soyayya daga nesan bai dade ba. A shekarar 1983, ya shaida mata: "Ina yawan tunaninki, duk da cewa a rude nake game da yadda nake ji a rai na."
"Kamar ba za mu taba so abin da ba za mu iya samu ba; wannan ne abin da ya hada mu; wannan ne abin da ya raba mu."
Neman hanyar da ta dace
A wata wasikar, matashi Obama ya yi rubutu yadda abokananshi ke neman yin aure ko kuma karbar ragamar kafanonin gidansu.
Amman domin an haife shi a Hawaii, mahaifi daga Kenya, kuma domin ya yi yawancin shekarun yarintan shi a Indonesiya, ya ji kanshi daban.
"Dole na ce na yi fama da hasada," in ji shi.
"Na samu kaina a wani halin da babu matsayi, tsari ko kuma al'ada wadda za ta tallafi mini, a iya cewa an yi mini zabin bin wata hanya ta daban ne.
"Hanya daya da zan iya bi in rage radadin kadaitar da nake ita ce in karbi al'adu da matsayi-matsayi sanna in mayar da su, ni kuma in zama nasu..."
Amman bai yi sauki ba.
A matsayinshi na dalibin da ya kammala karatun digiri a shekarar 1983, komawa Indonesiya inda ya girma, ya gane cewa shi ya zama bako a wannan kasar .
"Ba na iya magana da harshen kamar yadda nake yi da kyau a da.," in ji shi.
"Mutane suna mamaki na tare da mini biyayya da kuma mini dariya saboda ni Ba'amurke ba ne - kudi na da kuma tikitin jirgina na komawa sun danne kasancewa na baki."
Hoton shugaban kasa a matsayin matashi
Matashin da ya kammala karatun digiri ya san shi yana son ya yi aiki kan irin shirye-shiryen da ya zai zo ya tallafa wa a matsayinsa na shugaban kasa- amman ya sani, kamar sauran matasa, dole ya kasance ya yi abin da zai yiwu a lokacin.
"A mako daya na kasa biyan kudin tura takardar neman aiki a gidan waya, a makon da ya biyo baya kuma dole na rubuta cekin kudi na boge domin in yi hayan mawallafin rubutu na tafirata," kamar yadda ya rubuta a shekarar 1983.
"Albashi a kungiyoyin al'umma sun yi kadan wa bukatun mutum a halin yanzu, saboda haka ina ganin ina fatan samun wani aiki na yau da kullum saboda in tara isassun kudin da nake bukata domin in iya yin irin waddanan ayyukan kungiyoyin al'umma."
Da ya kama aiki a wani gidan wallafa littatafai, ya ce zama "daya daga cikin wadannan matasan wadanda ake ganin za su ci gaba kuma mutane suka yi ta yaba mini."
Amman ya yi fargabar cewa aikin babban kamfani ka iya gurbata dabi'unsa kuma ba da jimawa ba ya bar aikin.
Kuma akwai wasu alamu a rubuce-rubucensa da suka nuna irin mutumin da zai iya zamowa daga baya.
A wata wasikar da ya rubuta a shekarar 1984 ga Alexandra, ya yi tunani a kan abin da zai yi me zai yi da karin karfin fada-aji.
"Tunanina ba su kai karfin wadanda nake da su ba lokacin ina makaranta, amma suna tasiri lokacin da mutum ya dube su," in ji shi.
Source: BBC Hausa