Ganin cewa bai wuce shekara daya da rabi ba, a sake zaben shugabanni tun daga Majalisun Jihohi, Gwamnoni, Majalisun Tarayya, na Dattawa da kuma Shugaban Kasa, PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin alkiblar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa, INEC domin tsinkayen irin shirin da hukumar ta yi.
An kuma yi nazarin su kan su masu jefa kuri’u, domin sanin irin alkblar da suka dosa, irin zaman jiran da su ke yi ranakun sake zaben su zo, da kuma irin shirin su na yin amfanin da katin rajistar su, wanda shi ne ‘yancin su.
Tun bayan hawan sa kujerar shugabancin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sha nanatawa cewa zaben 2019 zai fi zabukan baya inganci. Wannan kuwa a bisa dukkan alamu ba za a yi mamaki ba, idan aka fara yin la’akari da cewa an yi zabukan cike gurbi da dama a karkashin Mahmood Yakubu, amma ba a samu yawan tashe-tashen hankula ba, kamar wasu zabuka da aka yi can shekarun baya.
Zaben da aka yi wa Yakubu a matsayin Shugaban Kungiyar Shugabannin Zaben Kasashen Afrika Ta Yamma, a baya bayan nan, ta kara tabbatar da nagartar shugaban na INEC. Baya ga wannan, zaben shi da aka yi ya jagoranci sa-ido wajen zaben kasar Liberiya, shi ma alama ce da ke nuna cewa an gamsu da INEC a Afrika ta yamma. Ga shi kuma an sake gayyatar sa da ya taimaka wajen ganin zabe mai zuwa na cikin watan Yunin 2017 a Cote d’Voire, ya samu gagarimar nasara.
To, kwanan nan kuma shugaban na INEC ya bayyana cewa hukumar sa za ta dauki masu aikin zabe na wucin gadi har milyan daya a zaben 2019.
Ko shakka babu, hakan na nuni da cewa ita dai INEC ta fara shiri kenan tun yanzu. Dama kuma Yakubu ya bayyana cewa ya koyi darasi daga zaben Liberiya, inda ya ce tuni da dadewa su ka fara shirin zaben, wanda aka gudanar ranar 10 Ga Oktoban da ya gabata.
Inda Gizo ke sakar, shi ne a wajen su jama’a masu jefa kuri’a. Tambaya a nan, shin idan ita INEC ta shirya, kuma kun shirya? Idan INEC ta fara shiri tun yanzu, ku ma kun fara shiri?
Duk ya waya dimbin al’ummar da ke Nijeriya, wadanda suka jefa kuri’a a zaben 2015 ba su kai milyan 40 ba. Wannan kuwa ya na nuna ragwanci ‘yan Najeriya wajen mikewa tsaye su tashi su nemi ‘yancin su ta hanyar zaben wanda su ke so ko wadanda su ke so su jagorance su a dimokradiyyance.
Abin mamaki ne mutum ya shekara huku ya na adawa da gwamnati, ya na hayagaga a gidajen radiyo da maciya ko cikin kasuwanni da sauran wuraren hira. Amma ba zai iya sadaukar da awa hudu daga cikin lokacin ba a ranar zabe ya je ya zabi wanda ya ke so.
A yau, jama’a maza da mata, manya da kanana, kowa ya koma sojan adawa ko kuma sojan kare gwamnati a soshiyal midiya. Tun daga wayewar gari, har karfe biyu na dare yawanci jama’a ana Facebook da WhatsApp da sauran zaurukan sada zumunta na soshiyal midiya ana tattauna batutuwa na siyasa.
A yau idan dan adawa ya shiga Facebook, zai nuna maka gwamnati mai ci, ko kuma wakilin sa bai tsinana musu komai ba. Amma a ranar zabe sai ka neme shi wurin jefa kuri’a ka rasa, ko sama ko kasa. Ya na can gindin radiyo ya na sauraren mahawara, kafin dare ya yi shi ma ya kafa tasa majalisar a yi ta mahawara.
Sai yaushe za a himmatu wajen yankar katin rajistar zabe? Sai yaushe kuma za a rika yi fitar farin-dango ana zuwa jefa kuri’a? Ku gane min hanya.
Source: Premium Hausa
Title :
Wani Shiri INEC Tayi Don Zaben 2019
Description : Ganin cewa bai wuce shekara daya da rabi ba, a sake zaben shugabanni tun daga Majalisun Jihohi, Gwamnoni, Majalisun Tarayya, na Dattawa da k...
Rating :
5