Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sanar cewa wasu mutane sun kashe wani dan sanda dake aikin faturo a hanyar Wuro-Dole-Pariya dake karamar hukumar Girei.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Othman Abubakar ya ce aukuwar wata ‘yar gadamace tsakanin dan sanda da wani fasinja ya yi sanadiyyar mutuwan dan sandan.
Koda yake Abubakar bai bada cikakken abin da ya tada gaddamar ba sai dai yace hayaniyar ta kaure ne tsakanin fasinjan da dan sandan bayan ya tsayar da su domin yayi bincike. daga nan sai musu ya kware tsakanin sa da wani fasinja a motar. Hakan bai yi ww dansandan dadi ba sai ya fusata ya ko dirka wa fasinjar harsahi a cikinsa.
Su kuma fasinjojin motan sai suka fusata suka hau dan sandan da duka sai da ya mutu.
Abubakar ya ce da suka zo daukar gawan dan sandan sun ga jikinsa da raunuka sannan sun tafi bindigarsa.
Bayan haka wani Sadiq wanda abin ya faru a gabansa ya ce ‘garin bada cin hancin Naira 50 ya sa aka sami wannan hargitsi da yayi sanadiyyar mutuwar fasinjar da dansandan.
Sadiq ya ce direban motan da fasinjan da aka harbe ne ya bada cin hancin Naira 50 wanda shi kuma dan sandan ya raina ya ce sai dai a bashi Naira 100.
” Da ganin haka fasinjan ya kwabi dan sandan akan dalilin karban cin hanci da yayi sannan harda neman kari .”
” Nan take ko dan sandan ya fusata ya daga ware bindigarsa ya ko seta ta a kan wannan fasinja sannan ya dirka masa a cikinsa. Su ko sauran fasinjojin ba suyi wata-wata ba suka hau wannan dan sanda da duka ta ko ina, daga karshe dai dan sandan ya mutu a wurin.
Source: Premium Hausa