A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina, daga sabon mukamin mukaddashin darakta a ma'aikatar harkokin cikin gida.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta fara neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 kan zargin yin sama da fadi da naira bliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon Najeriya.
A wancan lokacin har zanga-zanga wasu suka yi zuwa majalisar dokokin Najeriya domin nuna goyona baya ga Abdulrasheed Maina.
Amma bai fito ya kalubalanci neman da ake yi masa ba.
Bayan EFCC ta yi shelar nemansa ne aka daina jin duriyar Maina.
Ba a sake jin labarinsa ba sai lokacin da rahotanni suka ce ya koma aiki a ma'aikatar cikin gida ta Najeriya, a matsayin daraktan riko.
Amman ministan ma'aikatar cikin gidan, Abdulrahman Dambazau, ya ce shi bai san komai ba dangane da dawowar AbdulRasheed Maina aiki.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran ministan, Ehisienmen Osaigbovo, ya fitar ta ce daga ofishin shugaban ma'aikatan Najeriya ne aka turo Abdulrasheed aiki a ma'aikatar.
Saboda haka ministan bai san yaya aka yi Abdulrasheed Maina ya dawo ma'aikatarsa ba.
Mai magana yawun hukumar EFCC ya tabbatar da cewa, har yanzu hukumar tana neman AbdulRasheed Maina, ruwa-a-jallo.
Bugu da kari, sanarwar da hukumar EFCC ta bayar cewar tana neman Maina har yanzu tana nan a shafinta na Intanet.
Source: BBC Hausa
Title :
Wanene Abdulrasheed Maina?
Description : A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasar, AbdulRasheed ...
Rating :
5