Ana tsare da wani dan jarida na kasar Zimbabwe a kan wani labari da ke zargin cewa ana raba gwanjon rigunan mama da 'yan kamfai ga magoya bayan jam'iyyar Zanu-PF mai mulki a madadin Uwargidan shugaban kasar Grace Mugabe, in ji lauyoyinsa.
Suka ce mai yiwuwa ne dan jarida, Kenneth Nyangani ya fuskanci tuhume-tuhume kan laifin bata-suna.
Jaridar Newsday ta ruwaito cewa wani dan majalisa na jam'iyyar Zanu-PF, Esau Mupfumi ne yake raba kananan kayan matan kuma ya ce gudunmawa ce daga Grace Mugabe.
Hukumomi a kasar ba su ce uffan ba tukun game da batun kama dan jaridar.
Jaridar ta ce ba a san takamaimai wanda yake korafi a kan rahoton ba tsakanin shi dan majalisar ko kuma ita mai dakin shugaban kasa.
'Yan sanda a birnin Mutare na gabacin Zimbabwe ne suka kama Kenneth Nyangani a ranar Litinin da maryace bisa zargin "rubutawa da wallafa wani labari a kan kyautar tsoffin rigunan mama da kamfai" daga mai dakin shugaba Robert Mugabe a cewar wata sanarwa daga lauyoyin Kare Hakkin Dan'adam a Zimbabwe.
Jaridar mai zaman kanta tun da farko ta ruwaito cewa dan majalisar ya yi rabon kananan kayan matan a karshen mako ga magoya bayan jam'iyyar Zanu-PF a yankin Mutare.
"Na gana da Uwargida Grace Mugabe kuma an ba ni wadannan tufafi don na ba ku. Ga rigunan mama da 'yan kamfai nan an ba ku, an fada min cewa galibin naku ba su da kyau, don Allah ku zo ku karbi naku rabon yau," aka ambato Mista Mupfumi na cewa.
"Akwai kayan barci ma, ga takalman sandal da tufafi, duk ku zo ku karba, kyauta ce daga Uwargida Grace Mugabe," ya kara da cewa.
Tabarbarewar tattalin arziki a Zimbabwe ya tilasta wa mutane da yawa sayen gwanjo a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ya ce kayan gwanjon sun hadar da rigunan mama da singileti da 'yan kamfai daga kasashen Yamma wadanda ake kai wa kasar cikin sauki daga Mozambique.
Source: BBC Hausa
Title :
Uwargidan Shugaban Kasa Ta Raba Rigunan Mama
Description : Ana tsare da wani dan jarida na kasar Zimbabwe a kan wani labari da ke zargin cewa ana raba gwanjon rigunan mama da 'yan kamfai ga magoy...
Rating :
5