Mai rike da League Cup, Manchester United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe bayan da ta ci Swansea City 2-0 a karawar da suka yi a ranar Talata.
United wadda ta lashe kofin bara ta ci kwallonta biyu ne ta hannun Jesse Lingard daya kafin aje hutu, dayar kuwa bayan da aka dawo daga hutu.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga Arsenal ta doke Norwich City 2-1, Bournmouth ta ci Middlesbrough 3-1 da wasan da Bristol City ta doke Crystal Palace 4-1 da fafatawar da Leicester City ta ci Leeds United 3-1.
Sai a ranar Laraba ne Chelsea za ta kara da Everton da wasan da Tottenham za ta karbi bakuncin West Ham United.
Source: BBC Hausa
Title :
United Takai Mataki Na Gaba A Wasan League Cup
Description : Mai rike da League Cup, Manchester United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe bayan da ta ci Swansea City 2-0 a karawar da suka yi a ra...
Rating :
5