Shafin sada zumunta na Twitter zai kaddamar da wasu sabbin ka'idoji kan tallace-tallacen da ake yi a lokacin zabe.
Kamfanin Twitter ya ce ya dauki wannnan mataki ne domin maida martani kan sukar da aka rika yi game da kutsen da ake zargin Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na Amurka a shekarar 2016.
An dai gano wasu shafuka 200 masu alaka da gwamnatin Rasha
Amurka ta yi barazanar daukar mataki akan halayyar rashin gaskiya na kudaden da 'yan siyasa suke kashewa a shafukan sada zumunta.
A yanzu shafin Twitter zai dinga bada bayani a kan wanda ya biya kudin tallan da ya wallafa da yawan kudin da aka kashe da kuma masu amfani da shafin da ake son a ja hankalinsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Twitter Ta Fidda Sabbin Kaidojin Talla
Description : Shafin sada zumunta na Twitter zai kaddamar da wasu sabbin ka'idoji kan tallace-tallacen da ake yi a lokacin zabe. Kamfanin Twitter ya ...
Rating :
5