Tsoffafin mayaka a Ivory Coast suna shirin gudanar da wasu jerin zanga-zanga a fadin kasar yau.
Sun ce shugaban kasar Alassane Ouattarra ya kasa biyan kowannensu dala dubu ladan yakin da suka yi na tabbatar da shugaban ya dare karagar mulkin kasar.
Ba wannan ne karon farko a bana da wannan gwamantin ke fama da batun zanga-zanga da tsoffin mayaka ke gudanarwa ba na neman a biya su kudi.
A watan Mayu, fiye da sojoji dubu takwas rike da makamai suka dakatar da komai a kasar.
Yawancinsu tsoffin mayaka ne da aka shigar da su cikin sojin kasar, kuma suna ikirarin kowannen su na bin gwamnatin shugaba Alassan Ouattarra bashin fiye da dala 20,000 na shekarun da suka shafe suna kokarin dora shugaban a kan mulki.
A wancan lokacin, gwamnatin ta amince ta biya su, amma wannan lamarin ya janyo wata sabuwar matsala - akwai wasu tsoffin mayakan 6,000 da basu sami aikin soji ba dake neman a biya su kudade su ma.
Sun ce zanga-zangar ta yau domin iyalan wadanda suka mutu a cikinsu ne a yayin da ake yakin basasar kasar da kuma wadanda suka sami raunuka, kuma gwamnati ta manta dasu gaba daya.
Sun ce kuma suna da makamai, amma zasu gudanar da zanga-zangar cikin lumana - har sai an biya su kudadesu.
A nata bangaren, gwamnatin kasar ta ce tana tattaunawa da tsoffin mayakan.
Source: BBC Hausa
Title :
Tsofaffin Mayakan Ivory Cost Na Neman Hakkinsu
Description : Tsoffafin mayaka a Ivory Coast suna shirin gudanar da wasu jerin zanga-zanga a fadin kasar yau. Sun ce shugaban kasar Alassane Ouattarra ya...
Rating :
5