Wani masani kan harkar shirya fina-finai, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce daya daga cikin kalubalen da duniyar Kannywood ke fuskanta ita ce maimaita wasu tsirarun jarumai fiye da kima a fina-finai.
Farfesa Abdallah wanda shi ne shugaban Jami'ar Karatu Daga Gida Ta Najeriya, ya ce yawan maimaita wasu tsirarun jarumai ya sa finan-finan Hausa na Kannywood gundurar 'yan kallo.
A cewarsa, matukar ba a ba wa sabbin fuskoki dama suna nuna basirarsu, ta yaya su ma za su samu su bunkasa.
Farfesan wanda ya koyar da darasin tsara fina-finai a Jami'ar Bayero Kano ya ce basira da baiwa ba su takaita a wajen wasu tsirarun jarumai ba.
Su dai wasu fardusoshi a duniyar Kannywood na da ra'ayin cewa fina-finai ba su cika kasuwa ba, idan masu kallo suka ga bakuwar fuska a matsayin jarumi.
Sai dai Abdallah Adamu ya ce idan ka dauki fina-finan Amurkawa na Hollywood, za ka ga akasari jarumi daya ne yakan fito a cikin fim.
"Ka dauki kowanne jarumin Hollywood, babban jarumin Hollywood, kamar a ce Bruce Willis ko Arnold Schwarzenegger ko wani daban, za ka ga fim din sa da ya yi shi kadai ne ya fito."
A cewarsa hakan wata dama ce da ake ba wasu don ba da tasu gudunmawa su ma suna irin bajintarsu.
"Kowa Allah ya ba shi basirarsa saboda haka sai an gwada wadansu, idan kuma ba a gwada din ba, to ba za a samu nasara ba.
Manazarcin fina-finan ya ce mai yiwuwa abin da ya sa tsirarun jarumai suka kankane fina-finan Kannywood, shi ne akasari su ne suke shirya abubuwansu.
Ya ce da ana samun masu shirya fim daga wajen Kannywood da sun rika ba sabbin fuskoki dama don ciyar da harkar gaba.
Farfesa Abdallah Uba ya ce jami'arsa tana kokari don ganin ta fara kwas a kan harkar shirya fina-finai ta yadda ilmi a wannan fanni zai bunkasa
Source: BBC Hausa
Title :
Tsirarun Jarumai Sun Babbake Fina Finan Hausa
Description : Wani masani kan harkar shirya fina-finai, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce daya daga cikin kalubalen da duniyar Kannywood ke fuskanta ita ce...
Rating :
5