Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Liverpool da ci 4-1 a filin wasa na Wembley a gasar Premier.
Harry Kane ya fara zura wa Liverpool kwallo a raga minti hudu da fara wasan, daga nan ne Hugo Lloris ya ci wa Tottenham kwallo ta biyu a minti na 12.
A minti na 24 Salah ya farke wa Liverpool kwallo guda, wasan ya koma 3-1 ne yayin da Dele Alli ya ci tasa kwallon ana gab da zuwa hutun rafin loakci.
Bayan da aka dawo ne Kane ya kara cin kwallonsa ta biyu a wasan a minti na 56, inda wasa ya koma 4-1.
Sakamaon wasanya ya sa Tottenham ta koma maki 20 daidai da Manchester United wadda take mataki na biyu.
Source: BBC Hausa
Title :
Tottenham Ta Lallasa Liverpool
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa Liverpool da ci 4-1 a filin wasa na Wembley a gasar Premier. Harry Kane ya fara zura wa Liver...
Rating :
5