Takaddama ta kaure tsakanin Karamin Ministan Albakatun Man Najeriya Ibe Kachikwu da Shugaban Kamfanin Mai na kasar (NNPC) Mai Kanti Baru.
A wata wasikar da ministan ya aika wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ministan ya zargi shugaban kamfanin da "yin ba daidai ba da kuma rashin da'a."
A cikin wasikar da aka kwarmata ga jaridun Najeriya, ministan ya zargi Shugaban NNPC, Mai Kanti Baru da daukar manyan ma'aikatan kamfanin man da kuma ba da kwagilolin da suka haura dala biliyan 20.
"Sabanin yadda doka ta bukata wato sai ya nemi yardar karamin ministan," wanda shi ne shugaban hukumar da ke sa ido kan NNPC.
Hakazalika ministan ya ce "da na nemi sanin abin da ya sa shugaban NNPC din yin hakan, sai ya gaya mishi cewa shugaban kasan ne ya amince da daukar ayyukan da kuma ba da kwagilolin."
Sai dai kamfanin man bai ce komai ba tukuna.
Kodayake majalisar dattawan Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike da zai binciki zarge-zargen da ministan ya yi a cikin wasikar.
Takaddama tsakanin jami'an gwamnatin Buhari ba sabon abu ba ne.
A baya an taba samun takkadama tsakanin Ministan Shari'ar Kasar Abubakar Malami da kuma Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, sai dai dukkansu sun musanta zargin.
Hakazalika, an taba samun takaddama tsakanin Ministan Lafiya da kuma shugaban hukumar NHIS, wadda sai da ta kai ga dakatar da shugaban hukumar da kuma kafa kwamitin bincike kan al'amarin.
Source: BBC Hausa
Title :
Takaddama Ta Barke Tsakanin Karamin Ministan Mai Da NNPC
Description : Takaddama ta kaure tsakanin Karamin Ministan Albakatun Man Najeriya Ibe Kachikwu da Shugaban Kamfanin Mai na kasar (NNPC) Mai Kanti Baru. A...
Rating :
5