Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna gab da samun tikitin zuwa wasan cin kofin duniya wanda za a yi a badi a kasar Rasha.
A ranar Asabar ne Najeriya za ta kara da Zambia a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.
Idan Najeriya ta samu nasara a wasan, hakan yana nufin ke nan ta samu tikitin zuwa kasar cin kofin duniya wanda za a yi a shekarar 2018.
A karawar kasashen ta farko wanda kasar Zambia ta karbi bakunci, Najeriya ce ta samu nasara da ci 2-1.
Source: BBC Hausa
Title :
Super Eagles Na Gab Da Zuwa Russia 2018
Description : Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna gab da samun tikitin zuwa wasan cin kofin duniya wanda za a yi a badi a kasar Rasha. A ranar Asabar...
Rating :
5