Wasu bayanan sirri na rundunar sojin saman Najeriya sun nuna cewa an kashe matar shugaban kungiyar Boko Haram, Malama Firdausi Shekau, a wasu hare-haren sama da aka kai yankunan Durwawa a wajen garin Urga da ke kusa da Konduga a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojin sama ta aikewa manema labarai a ranar Laraba, wadda mai magana da yawunta Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya sanyawa hannu.
Sai dai babu wata majiya mai karfi zuwa yanzu da ta tabbatar da ikirarin nasu.
Ko a baya ma rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa ta kashe manyan kwamandojin Boko Haram har ma da shugabansu Abubakar Shekau, sai dai daga baya kungiyar ta musanta.
Rundunar ta ce rahotanni sun nuna cewa Malama Firdausi na wakiltar mijinta ne a jan ragamar wani taro da sauran mayakan kungiyar ke halarta a wajen da aka kai hare-haren saman.
A ranar 19 ga watan Oktobar 2017 ma rundunar sojin kasar ta ce ta samu nasara a wani hari da ta kai kan wasu wurare da suka kasance maboyar mayakan Boko Haram din a Durwawa.
Rahoton da aka tattara na ta'adin da aka yi a lokacin ya nuna cewa harin saman da aka kai ya sa wuta ta tashi, abin da ya lalata wasu gine-gine na mayakan Boko Haram inda da dama suka mutu, ya kuma tilasta wa kadan daga cikin su tserewa.
Dama dai rundunar sojin kasan ta fitar da sanarwar cewa ta fara wani aiki na kai wa mayakan Boko Haram hare-hare ta sama, da ta yi wa lakabi da Operation Ruwan Wuta.
An fara aikin Operation Ruwan Wuta ne a ranar Litinin 23 ga watan Oktobar 2017, don yin ruwan wuta a maboyar mayakan Boko Haram.
A ranar farko ta fara aikin, rundunar sojin saman ta yi ruwan wuta sosai a wasu yankuna da ke garin Garin Maloma.
An yi amfani da jiragen yaki biyu masu dauke da bama-bamai da rokoki inda aka dinga luguden wuta, aka kuma kwashe wasu mayakan masu kokarin tserewa.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojin Nijeriya Sunkashe Matan Shekau A Wani Luguden Wutan
Description : Wasu bayanan sirri na rundunar sojin saman Najeriya sun nuna cewa an kashe matar shugaban kungiyar Boko Haram, Malama Firdausi Shekau, a was...
Rating :
5