Hafsan hafsoshin rundunar sojojin Amurkan ya ce sojojin kasar za su ci gaba da taimakawa sojojin Nijar - duk da mutuwar sojojin Amurkan guda hudu, wanda ya hada da Saje Johnson a wani harin kwanton bauna da aka yi musu.
Janar Joseph Dunford, ya ce ana binciken sanadiyyar mutuwar sojojin na Amurka.
Mako uku bayan harin da aka akai a Nijar, ya nuna damuwarsa game da lamarin, inda ya ce akwai bukatar a samu amsoshi dangane da aikin da suke yi a cikin kasar.
Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe sojoji uku ne ranar 4 ga watan Oktoba, inda aka raunata wasu biyun bayan da aka yi musu kwanton bauna a lokacin da suka ayyukan bincike akan iyakar kasar da Mali.
Sojojin na Amurka sun ce 'yan bindiga ne masu alaka da kungiyar IS ne suka kai wannan harin.
Janar Dunford ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne a sanadiyyar musayar wuta tsakanin su da maharan, kuma "sun sami kansu a cikin wani mawuyacin hali", inji shi.
Sai bayan sa'a guda da fara batakashin sannan sojojin na Amurka suka nemi taimako.
Har ila yau an aika da jiragen Faransa wurin, inda daga baya aka dawo da gawarwakin sojojin Amurka uku daga wurin -- amma ba a ga gawar Saje Johnson ba sai ranar 6 ga watan Oktoba. Janar Dunford ya ce masu bincike na tattara bayanai domin sanin yadda lamarin ya faru:
Ya ce: "Dole mu sanar da iyalan sojin da suka mutu dukkan bayanai game da abin da ya faru, kuma 'yan Amurka zasu so sanin abin da sojojinsu keyi a wannan kasa a wannan lokaci".
Janar Dunford ya bayyana cewa sojojin Amurka sun shafe fiye da shekara 20 a Nijar, inda a halin yanzu kimanin sojoji 800 ne ke ayyukan taimako ga wata tawaga ta dakarun Faransa masu yaki da kungiyar IS da ta al-Qaida da 'yan kungiyar Boko Haram a yankin Afirka ta yamma.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojin Amurka Bazasu Fice Daga Nijar Ba
Description : Hafsan hafsoshin rundunar sojojin Amurkan ya ce sojojin kasar za su ci gaba da taimakawa sojojin Nijar - duk da mutuwar sojojin Amurkan guda...
Rating :
5