Tun bayan da badakalar yin lalata da mata 'yan fim din Amurka, wacce ta shafi fitaccen mai shirya fina-finan Hollywood, Harvey Weinstein, ta bayyana bangarorin fina-finai daban-daban na duniya ke aza alamar tambaya: shin ana samun irin wannan batu a bangarorinsu?
Fitattun jarumai mata irinsu Ashley Judd da Angelina Jolie da kuma Gwyneth Paltrow sun zargi Mr Weinstein da yin lalata da su kafin ya sanya su a cikin fina-finansa.
Jarumai mata fiye da 40 ne suka fito fili suka bayyana cewa fitaccen furodusan ya yi lalata da su tun bayan da jaridar The New York Times ta soma kwarmata batun ranar biyar ga watan Oktoba.
Sai dai Mr Harvey, wanda da farko ya musanta zargin, ya ce ya yi lalatar da su ne tare da amincewarsu.
Tuni dai 'yan sandan birnin New York da London suka soma gudanar da bincike kan lamarin.
Me ake ciki a Kannywood?
An dade ana yi wa masu yin fina-finan Kannywood kallo a matsayin mutanen da ke bata tarbiyar al'umma.
Kazalika ana yi musu duba na mutanen da ke aikata masha'a kamar zinace-zinace da yin luwadi da sauransu.
Sai dai sun sha musanta wannan zargi.
A shekarun baya, wani bidiyo da ya bayyana na wata tsohuwar 'yar fim inda wani ke lalata da ita, ya jawo wa 'yan Kannywood matukar bakin jini, lamarin da ya sa gwamnatin Kano ta wancan lokaci ta haramta yin fim a jihar.
Hukumar da ke tace fina-finai ta lokacin ta matsawa masu yin fim abin da ya kai ga durkushewar kusan daukacin masu harkar fim.
Daga baya dai al'amura sun daidaita, kuma ko da yake babu wata 'yar fim da ta fito fili ta ce wani furodusa ko kuma babba da ke cikin harkar ya taba neman yin lalata da ita, rahotanni da dama na cewa hakan na faruwa.
Sai dai rahotannin sun nuna cewa mata 'yan fim na jin tsoron fitowa fili su fadi abin da ke cikinsu game da zargin yi musu lalata ne saboda, a Musulince, irin wannan zargi na bukatar kwakkwarar shaida kafin a amince da shi.
Wata fitacciyar jaruma ta taba shaida min cewa manyan masu ruwa da tsaki da dama sun nemi yin lalata da ita amma ta ki yarda.
Jarumar, wacce ba ta so na ambaci sunanta, ta shaida min cewa "Wallahi mutanen da nake gani da mutunci a harkar Kannywood ba su da yawa domin kusan kowa ka ce kana son shiga fim dinsa sai ya nemi ya yi lalata da kai".
Ta kara da cewa Jarumi Ali Nuhu ne kawai bai taba nuna son yin lalata da ita ba.
Daya daga cikin jaruman mata, Hauwa Waraka, ta shaida wa BBC cewa ko da yake babu wani da ya taba bukatar ta yi lalata da shi kafin ya saka ta a fim dinsa, ba za ta kawar da yiwuwar cewa hakan na faruwa ba.
"Ni dai babu wanda ya taba bukatar na yi lalata da shi kuma ban san wata da ta ce wani ya taba son yin lalata da ita ba. Sai dai ka san wannan harkar kowa da halinsa ya zo, babu wanda za ka bayar da shaida a kansa".
Ta kara da cewa: "Su matan da suke indostri din ai ba yara ba ne, ba yadda za a yi a ce za a kama a neme su da karfi, dole sai sun yarda, don haka duk abin da ki ka ga an yi a harkar nan mutum shi ya so."
Da alama wannan batu nata na da alamun gaskiya saboda wani darakta ya shaida min cewa irin badakalar da ke faruwa a Kannywood ta sa "nake janye jikina daga cikinta."
Sai dai da BBC ta tuntubi Ali Nuhu kan wannan batu ya musanta faruwar hakan, yana mai cewa a duk shekarun da ya kwashe cikin harkokin fim din Kannywood bai taba ganin wacce ta ce an yi lalata da ita ba.
"Ni gaskiya ba taba samun wacce ta ce an yi lalata da ita kafin a sa ta a fim ba, kuma ina ganin wannan zargi ba gaskiya ba ne domin kuwa mu muna kokarin kare addini da al'adunmu ne. Akwai kwamiti da ke sanya ido kan masu neman yin lalata da 'yan fim da ma kula da yadda muke harkokinmu".
Shi ma fitaccen daraktan fina-finan na Kannywood, Mallam Aminu Saira ya shaida BBC a kwanakin baya cewa bai taba neman yin lalata da mace kafin ya sanya ta a fim dinsa ba.
A cewarsa, "Wannan batu ba gaskiya ba ne; hasalima wanna ne karo na farko da aka yi min irin wannan tambayar kuma ina gani da a ce ana samun irin wannan lalata da 'yan matan fim da suka gabata sun yi korafi. kar ka manta wasu 'yan fim mata sun yi aure. Da a ce haka batun yake da idan wasu sun yi shiru, wasu sai sun yi magana".
Da alama dai zarge-zargen yin lalata da kuma bata tarbiya za su ci gaba da mamaye harkokin fina-finai, ba kawai na Kannywood ba, har da na Nollywood da Bollywood da sauransu saboda yadda wadannan bangarori suka zama tamkar hatsin-bara.
Source: BBC Hausa
Title :
Shin Anayin Lalata Da 'Yan Matan Kannywood?
Description : Tun bayan da badakalar yin lalata da mata 'yan fim din Amurka, wacce ta shafi fitaccen mai shirya fina-finan Hollywood, Harvey Weinstein...
Rating :
5