Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya gwale takwaransa na Amurka, Rex Tillerson, inda ya ce ba don 'yan Shi'a ba da yanzu IS ta kwace Syria da Iraqi.
Ya ce 'yan Shi'an Iran da Iraqi sun sadaukar da rayukansu wajen hana mayakan IS karbe iko da birnin Bagadaza na Iraqi da Damascus a Syria.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce kamata ya yi sojojin sa-kai masu samun goyon bayan Iran da ke taimaka wa yaki da kungiyar IS su kwance damara ko su koma gida Iran yanzu, don kuwa yakin ya kusa zuwa karshe.
Mista Tillerson ya yi wannan jawabi ne a yankin Gulf yayin wata ziyara wadda a wani bangare ke kokarin dakile karuwar fada-a-jin Iran a Gabas ta Tsakiya.
Wata wakiliyar BBC ta ce Amurka na bayyana damuwar cewa Iran za ta yi amfani da damar nasarar da aka samu a kan IS wajen fadada tasirinta a kasashen Iraqi da Syria.
Dakarun gwamnatin Iraqi da ke samun goyon bayan Amurka sun yi yaki da mayakan IS tare da gamayyar akasari 'yan Shi'a mai suna Popular Mobilisation Units (PMU), mai samun goyon baya da kudade daga Iran.
Ana zargin wasu 'yan kungiyar PMU da cin zarafin fararen hula 'yan Sunni, ciki har da amfani da azabtarwa da kashe-kashe, yayin fafatawa a baya don kwato yankunan da mayakan suka mamaye a Iraqi.
Haka zalika, sojojin sa-kan sun shiga fadan da aka fafata a makon jiya don kwace yankunan da ke karkashin Kurdawa tun a shekara ta 2014, lokacin da IS ta mamaye arewacin Iraqi sa'ad da rundunar Iraqi ta karye.
Source: BBC Hausa
Title :
'Yan Shia Ne Suka Hana Kwace Iraqi Daga Syria-Iran
Description : Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya gwale takwaransa na Amurka, Rex Tillerson, inda ya ce ba don 'yan Shi'a ba da y...
Rating :
5