Yayin da ta kwashe kusan dukkan rayuwarta a karuwanci a kasar New Zealand, Sabrinna Valisce ta kasance mai gwagwarmayar tabbatar da halascin aikin karuwanci.
To amma yanzu ta sauya ra'ayinta game da wannan kuduri, a maimakon hakan yanzu kira take yi da a gurfanar da mazaje masu amfani da karuwai a gaban kotun.
Mahaifin Sabrinna Valisce ya kashe kansa yayin da take 'yar shekara 12, hakan ne kuma ya sauya ilahirin rayuwarta.
Cikin shakara biyu, mahaifiyarta ta sake wani auren inda kuma suka fice daga kasar Australiya zuwa birnin Wellington, na kasar New Zealand, inda a can ne rayuwarta ta gurbace.
Valisce ta ce "na yi matukar bakin ciki saboda mijin mahaifiyata mutum ne mafadaci, kuma ba wanda zan iya yi wa magana."
Ta yi burin zama kwararriyar mai rawa, inda kuma ta kafa wata kungiyar koyar da rawa a makarantar da take, wacce kuma ta samu karbuwa sosai a makarantar.
To amma a cikin 'yan watanni ta tsinci kanta a kan tituna, inda take karuwanci domin samun abin da za ta tallafi da rayuwarta.
Yayin da take tafiya zuwa makaranta daga gidansu, wani mutum ya yi mata tayin zai ba ta dala 100 domin yin lalata da ita.
Ta ce, "Ina sanye da kayan makaranta, don haka ya sani sarai ni yarinya ce."
Valisce ta yi amfani da kudin wajen guduwa zuwa birnin Auckland, inda ta fara tambayar cibiyar karuwanci ta YMCA.
"Na yi kokarin neman taimakon wani ta hanyar kiran waya, yayin da nake wajen dakunan kwanan dalibai, to amma ana amfani da wayar, don haka dole na jira," in ji ta.
"'Yan sanda sun tsaya kuma suka tambayeni me nake yi. Sai na ce musu ina jira ne zan buga waya.
"Sun bincike ni game da kwaroron-roba, inda suke tunanin cewa ni karuwa ce, saboda cibiyar karuwanci ta YMCA na bayan titin Karangahape, wani yanki da karuwai ke cin karensu-babu-babbaka.
"Abin mamaki hakan ne ma ya bani damar zuwa yankin domin samun kudi. 'Yan sandan sun yi ta razana ni, to amma nasan cewa zan ci gaba da gararamba a kan titi idan har bani da masu-gida-rana.
Daga nan sai Valisce ta nufi titin Karangahape, ta kuma nemi shawarar wata mata da ke aiki a wajen.
Ta nuna wa Valisce wurare biyu da za ta iya yin aiki, "ta kuma bani kwaroron-roba, tare da gaya min kudin da zan rika biyanta ta kuma bani shawarwarin yadda zan yi amfani da su wajen samun karbuwa a sana'ar, da kuma kaucewa samun matsala da abokan huldata.
"Gaskiya ta burgeni. Duk da cewa Samoan ta yi kankanta a wajen, amma kuma kamar ta dauki dogon lokaci a wajen."
Bayan shafe shekara biyu tana yawo a kan tituna, a shekarar 1989 sai Valisce ta ziyarci cibiyar karuwancin New zealand wato (NZPC) da ke birnin Christchurch.
Ta ce: " Ina neman taimako ne, domin barin karuwanci, to amma abin da kawai nake yi shi ne rabar da kwaroron-roba.
An kuma gayyaceta zuwa gidan raye-raye da sharholiya a lokacin wani bikin shakatawa a dararen Juma'a.
Valisce ta ce tana iya tunawa cewa, "Sun fara magana game da yadda ake tsangwamar karuwai, shi ne babban kalubalen aikin, kuma karuwanci sana'a ce kamar ko wacce sana'a."
Ta kasance cikakkiyar kawaliya kuma mai goyon bayan kiran halasta ayyukan karuwanci da kuma kawalci.
"Na ji kamar wani sauyi ne ya tinkaro. Na yi farin ciki dangane da yadda halasta karuwancin zai kawo wa mata sauki a rayuwarsu," in ji ta.
An halasta karuwancin a shekarar 2003, kuma Valisce ta halacci bikin da cibiyar karuwancin ta shirya.
Dokar sauya fasalin karuwanci ta bai wa gidajen karuwai damar zama halattattun wuraren kasuwanci, sabuwar dokar ta bai wa mata damar zabin kariya ga kawunansu.
Ta ce: "Na yi tunanin hakan zai bai wa mata karfi da 'yanci, amma daga baya na gano akasin hakan ne daidai."
Matsala daya ita ce dokar ta bai wa masu gidajen karuwai damar bude yin caca a wata yarjejeniya, inda za su biya wasu kudade domin yin duk abin da suke son yi da matan.
Valisce mai shekara 40 ta nufi wani gidan karuwai da ke birnin na Wellington domin neman aiki, ta kuma firgita da abin da ta gani.
"A ranata ta farko, na ga wata yarinya ta dawo cikin wani mummunan yanayi, tana kuka da rawar jiki, ta kuma kasa yin magana.
"Mai maraba da bakin nata yi mata fada, tana ce mata ta koma bakin aiki. Daga nan sai na kwashi 'yan tsummokaraina na kara gaba," in ji ta
A yayin da take aikin wucin gadi a nan, ta fara tunanin zama mai hani da aikata karuwanci.
Ta bar aikin karuwanci a farkon shekarar 2011, inda kuma ta tafi yankin gabar tekun Queensland a Australia, domin samun sabuwar alkiblar rayuwa, to sai dai tana cike da rashin jin dadi.
Lokacin da wata makwabciyarta ta yi kokarin daukarta aikin karuwanci, sai ta ki amincewa, "na ji kamar an dora min dutse a goshina. Ya aka yi ta tambayeni? Na san cewa kawai saboda ta ga ni mace ce shi ne kawai dalilin," in ji Valisce.
Daga nan kuma duk lokacin da makociyar tata ta ganta sai ta zageta.
Valisce ta fara haduwa da mata a shafukan sada zumunta, matayen da ke goyon bayan haramta karuwanci inda suka kira kansu da masu hani da aikata karuwanci.
Valisce ta kafa wata kungiya mai suna Australian Radical Feminists, kuma daga baya an gayyaceta zuwa wani taro da aka gudanar a jami'ar Melbourne a shekarar da ta gabata, shi ne taro na farko da ke hana karuwanci da a ka gudanar a kasar Australia, inda jahohi da dama suka halasta gidajen karuwai.
Shi kansa birnin na Melbourne ya halasata gidajen karuwai tun tsakiyar shekarun 1980, kuma hakan na samun goyon baya daga mutanen kasar, duk da haka kuma akwai kungiyoyin da ke adawa da wannan mataki.
Ta bayyana wannan lokaci, yayin da ta fara zama mai fafutikar hana karuwanci, ta kuma fara jin nutsuwa game da abin da ta aikata a baya, "yayin da nake fara sabuwar rayuwar"
"Na fara cire abin a raina da jikina sannan kuma daga tunanina," in ji ta.
Bayan taron Valisce ta je wajen likita an kuma yi mata gwajin damuwa a ranta.
Ta ce, "Sakamakon lokacin da na dauka n-ina karuwanci, abin ya shafi rayuwata, amma na yi nasarar kubucewa duk illolin."
A ganin Valisce, babban maganin abin shi ne aiki da matan da suka fahimci dalilin da ya sa mata ke shiga aikin karuwanci, da kuma wadanda ke kira da a haramta karuwancin gaba daya.
Tana kuma son tabbatar da cewa matan da suke shiru-shiru game da masu muzguna musu sun samu bakin yin magana.
"Ba wai burina shi ne kama matan da ke wannan sana'a ko kuma hana su ba, amma ina so in kawo sauyi kuma wannan na bukatar yin magana, iya iyawata, domin taimaka wa sauran mata." in ji ta.
Source: BBC Hausa