Tsohon gwamnan jihar Sakkwato a Najeriya Aliyu Magatakarda Wamakko, ya tsallake rijiya da baya ranar Lahadi da daddare, bayan wani sashe na gidansa ya rufta.
Mai magana da yawun Sanata Wamakko, wanda a yanzu dan majalisar dattawan kasar ne, ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni.
Alhaji Bashir Mani ya ce lamarin ya faru ne jim kadan da ficewar Sanata Wamakko daga gidan wanda ke a unguwar masu-hannu-da-shuni ta Gawon-nama; bayan kammala wata ganawa da 'yan siyasa da ya yi a gidan.
Sai dai wata majiya daga iyalan Sanata Wamakkon ta ce yana cikin gidan lokacin da abun ya faru, sai dai ba a sashen da yake ba ne ruftawar ginin ta afku.
"Hakan ne ya sa ba a fi minti goma ba sai ga Gwamna Aminu Tambuwal ya iso gidan da sauri saboda yadda labari ya bazu cewa ginin ya rufta da shi a ciki," in ji wani makusancin tsohon gwamnan na jihar Sakkwato.
Alhaji Bashir Mani ya ce babu kowa a sashen ginin da ya rufta din lokacin da lamarin ya faru domin ana gyaran sashen ne.
Source: BBC Hausa
Title :
Sanata Wamakko Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Description : Tsohon gwamnan jihar Sakkwato a Najeriya Aliyu Magatakarda Wamakko, ya tsallake rijiya da baya ranar Lahadi da daddare, bayan wani sashe na ...
Rating :
5