Dan wasan Liverpool, Sadio Mane zai yi jinyar mako shida, sakamakon raunin da ya yi a lokacin da ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Senegal tamaula.
Senegal ta sauya Mane mai shekara 25 saura minti daya a tashi daga fafatawar a karawar da ta ci Cape Verde 2-0 a wasan shiga gasar cin kofin duniya a ranar Asabar.
Dan kwallon ba zai buga wa Liverpool wasan da za ta yi da Manchester United da Tottenham a gasar Premier da gasar Zakarun Turai da kungiyar za ta yi da Maribor.
Tun farko hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da Mane daga buga wasa uku, bayan da aka ba shi jan kati a karawar da Manchester City ta doke Liverpool 5-0 a gasar Premier.
Mane ya ci wa Liverpool kwallo uku a wasa biyar da ya fafata a kakar bana.
Senegal wacce ke mataki na daya a rukuni na hudu za ta kara da Afirka ta Kudu a ranar 10 da kuma 14 ga watan Nuwamba, kuma Mane ba zai buga wasan ba.
Source:BBC Hausa
Title :
Sadiyo Mane Zaiyi Jinyar Sati Shida
Description : Dan wasan Liverpool, Sadio Mane zai yi jinyar mako shida, sakamakon raunin da ya yi a lokacin da ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Senegal ...
Rating :
5