Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da shawarar amfani da wata sabuwar allurar riga-kafin zazzabin taifod, wadda za a rika amfani da ita.
Kwararru sun yi amanna cewa, idan har allurar riga-kafin ta yi matukar tasiri, za ta taimaka wajen kawar da cutar baki daya.
Sabanin sauran alluran riga-kafin, sabon maganin yana amfani ga yara kanana, wadanda ke matukar fuskantar hadarin kamuwa da cutar.
An yi kiyasin zazzabin na taifod yana halaka mutane fiye da dubu dari biyu a sassan duniya a duk shekara.
Kwayar cutar Salmonella Typhi ce ke haddasa zazzabin taifod .
Alamun cutar sun hada da
1 Zazzabi da zafin jiki
2 Ciwon kai
3 Amai gudawa
4 Rashin cin abinci.
Kwayar cutar na saurin yaduwa a gurbattaccen ruwan sha ko kuma abinci.
Cutar ta fi kamari a kasashen da ba su da tsafattacen muhali da kuma ruwan sha musaman a Asiya da kuma yankin kudu da sahara na Afrika.
Source: BBC Hausa
Title :
Sabuwar Rigakafin Cutar Typhoid
Description : Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da shawarar amfani da wata sabuwar allurar riga-kafin zazzabin taifod, wadda za a rika amfani da ita. Kwa...
Rating :
5