Shugaban kula da hurda da jama’a na rundunar sojn sama Olatokunbo Adesanya ya ce sun sami nasaran tarwatsa wasu mabuyan Boko Haram dake Urga kusa da Konduga a Barno.
Da yake fadin haka ga manema labarai a Abuja Olatokubo ya ce jiragen saman yakin rundunar ne ta yi ta kai hari wasu maboyan Boko Haram don hana su ci gaba da gudanar da ayyukan su daga irin wadannan wurare.
Ya ce sanadiyyar haka sun tarwatsa su sannan da yawa daga cikin su sun gudu da raunuka.
” Mun kai wannan hari ne bayan samun bayannan sirri da muka samu kan wadan su maboyan ‘yan Boko Haram a wadannan wurare. “
Source: Premium Hausa
Title :
Rundunar Sojin Sama Sunyi Wa Maboyan Boko Haram Ruwan Bama Bamai
Description : Shugaban kula da hurda da jama’a na rundunar sojn sama Olatokunbo Adesanya ya ce sun sami nasaran tarwatsa wasu mabuyan Boko Haram dake Urga...
Rating :
5