Cristiano Ronaldo zai je gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi, bayan da Portugal ta ci Switzerland 2-0 a karawar da suka yi a Lisborn a ranar Talata.
Switzerland ce ta fara cin gida ta hannun Johan Djourou daga baya Portugal ta kara ta biyu ta hannun Andre Silva.
Wannan sakamakon ne ya sa Portugal ta yi ta daya a rukuni na biyu, ita ma kasar Faransa ta kai gasar cin kofin duniya bayan da ta ci Belarus 2-1.
Sweden ce ta yi ta biyu a rukunin farko duk da doke ta 2-0 da Netherlands ta yi a ranar Talata.
Hakan na nufin Netherlands ba za ta je gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018 ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Zaije Gasan Kofin Duniya A Rasha
Description : Cristiano Ronaldo zai je gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi, bayan da Portugal ta ci Switzerland 2-0 a karawar da suka yi a Li...
Rating :
5