Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa akan yadda ake cigaba da samun korafe korafe kan batun albashin ma'aikata a jihohin kasar.
Shugaban ya ce abin takaice ne cewa wasu jihohi sun kasa sauke nauyin da ke kansu na biyan aklbashin ma'aikata duk da makudan kudin da gwamnatinsa ta baiwa jihohin domin su biya ma'aikata hakkokinsu.
Shugaba Buhari ya ce rabin na daure masa kai yadda ma'aikata a jihohi ke iya daukan dawainiyar iyalansu su ciyar da su, kana su biya musu kudin makaranta duk da cewa gwamnonin basa biyansu albashi a kan lokaci.
Ya kuma ce da mamaki gwamna ya iya barci duk da cewa bai biya ma'aikata albashinsu ba na tsawon watanni.
Ya ce da bukatar a sake lale domin ganin an warware matsalar.
Amma shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce lamarin ya sha karfin gwamnonin ne saboda yawancinsu sun gaji matsalolin ne daga hannun tsofaffin gwamnoni a shekarar 2015.
Wannan matsalar ta rashin biyan albashi tayi kamari a Najeriya, a inda a wasu lokutan har ta kan kashe auren wadanda lamarin ya shafa.
Masu sharhi na ganin cewa duk da wadannan matsalolin, gwamnonin kasar basu daina gudanar da rayuwa irin ta kasaita ba da kuma almubazzaranci da dukiyar al'umma.
Source: BBC Hausa
Title :
Rashin Biyan Ma'aikata Albashi Yanaban Takaici-Buhari
Description : Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa akan yadda ake cigaba da samun korafe korafe kan batun albashin ma'aikata a jihohin k...
Rating :
5