Shahararriyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.
Wannan batu ne ya jawo kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa reshen jihar Kano, MOPPAN, ta koreta daga masana'antar a watan Oktoban bara.
A wata wasikar da ta aike wa MOPPAN, wacce BBC Hausa ta samu kwafi, Rahama ta nemi afuwa kan abin da ta yi, tana mai cewa "kuskure ne," kuma za ta "kiyaye gaba".
Jarumar, wacce korar tata ta sa ta koma fitowa a fina-finan Nollywood, ta kuma tabbatarwa da Nasidi Adamu Yahayacewa hakika ta nefmi gafara" kan rungumar mawaki Classiq da ta yi.
Sai dai wannan wasika da Rahama ta rubuta tamkar ta yi amai ta lashe ne, saboda ko a watan Yulin da ya gabata ta shaida wa BBC cewa babu wanda ya dakatar da ita daga Kannywood.
Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema bayan sun tattauna a hukumance.
Amma ya ce kungiyar za ta yi kokarin kwatanta adalci ga Rahama kan duk wani mataki da za su dauka.
Ba wanda ya dakatar da ni- Rahama Sadau
Abin da wasikar ta kunsa
Ta rubuta cewa: "An kai shekara daya kenan tun faruwar wannan lamari, na yi iyakar kokarina don na nutsu sosai ta yadda ba za a bai wa kalamaina wata ma'ana ta daban ba kamar yadda kafofin yada labarai da wasu mutane suka dinga yi a baya."
"Ni 'yar adam ce wacce ba ta kubuta daga aikata kuskure ba, kuma ni 'ya ce wadda za a iya yi wa gyara, ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu shirya fina-finai, da dukkan al'ummar arewacin Najeriya da ma dukkan masu kallo da su gafarce ni," in ji Rahama.
Kazalika, jarumar ta yi magana a wasu gidajen rediyo na jihar Kano, inda ta jaddada neman gafarar musamman ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da kuma gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje.
A karshen wasikar dai Rahama ta yi alkawarin bin dokokin da kungiyar ta shimfida.
Source: BBC Hausa
Title :
Rahma Sadau Tanemi Gafaran Ganduje Da Sarki Sunusi Na Biyu
Description : Shahararriyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da...
Rating :
5