Kulob din Everton ya kori Ronald Koeman ranar Litinin bayan da Arsenal ta doke su a gasar Firimiya.
Rashin nasarar ya jefa kungiyar sahun kulob uku da ka iya faduwa a gasar idan suka kare a haka.
Tsohon dan wasan na Ingila Naville, mai shekara 40, ya taka-leda fiye da sau 250 a Everton a shekara takwas da ya shafe a kulob din.
A baya ya taba zamowa mataimakin koci a kungiyar Valencia ta La Ligar kasar Spaniya.
A ranar Talata ne Everton ta tabbatar da cewa kocin tawagar 'yan kasa da shekara 23 David Unsworth zai ci gaba da jan ragamar kulob din a matsayin riko.
Zai kuma fara jan ragamar kulob din a wasan da za su yi ranar Laraba a gasar cin kofin Carabou da Chelsea.
Rahotanni sun nuna cewa Ryan Giggs ma ya nuna sha'awarsa kan aikin, hakazalika ana kuma alakanta kocin Burnley Sean Dyche da tsohon manajan Bayern Munich Carlo Ancelotti da aikin na Everton.
Source:BBC Hausa
Title :
Phil Neville Nason Karban Kocin Everton
Description : Kulob din Everton ya kori Ronald Koeman ranar Litinin bayan da Arsenal ta doke su a gasar Firimiya. Rashin nasarar ya jefa kungiyar sahun k...
Rating :
5