Fitowar da Gwamnan jihar Ekiti ya yi, inda ya kada gangar neman takarar shugabancin kasar nan a 2019, karkashin jam’iyyar PDP ya tayar da kura a kasar nan, musamman a Arewa.
Duk da cewa jam’iyyar ta fito ita ma ta sacce tayar motar Ayo Fayose cewa kada ya bata lokacin sa, an bada takarar ga Arewa, hakan bai hana shi nuna cewa da gaske yake yi ba, kuma bai hana wasu nuna goyon bayan sa ba.
Kwatsam sai kuma ga shi tsohon minista kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato, Damishi Sango, ya fito a farkon makonnan ya ce Fayose ya fusata ne ya fito takara saboda ya ga wadanda ke da hakkin su fito takarar, sun nuna kamar ba da gaske su ke yi ba. Sango dai ya na nufin ‘yan Arewa kenan.
Wani abin lura shi ne, kalamin Sango da ya ce tun yanzu ya kamata masu sha’awar takara su fito su fara motsawa, domin ko ba komai, ita kan ta jam’iyyar PDP za ta kara karsashi kuma ya kasance kamar an yayyafa mata ruwan farkawa ta mike da karfin ta.
A fili ta ke cewa akwai masu son fitowa takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, amma dai duk a cikin su, babu wanda ya nuna da gaske ya ke yi, kamar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Jama’a da yawa na ganin cewa Lamido ne kadai zai iya nasara a kokuwar 2019, ganin cewa har yanzu APC kamar ta na dawurwura a wuri daya ne.
Batun cin hanci da rashawa da APC ta yi rantsuwar kawar da shi, da zarar ta hau mulki, abin na neman ya zama rantsuwar kaffara, domin na farko dai sama da shekaru biyu kenan, har yau ba a daure ko da wani tsohon gwamna ko tsohon ministan da aka yi wa korar-kare a zaben 2019 aka rika kiran su barayi ba.
Sannan kuma su kan su jami’an wannan gwamnatin, ana yi wa da yawan su kallon cewa su din ma ashe ba mutane ba ne, mutum-mutumi ne, domin ana yi musu zargin harkalla, kashe-mu-raba, dakasharama da cuwa-cuwa, irin wadda su ka yi rantsuwar za su kakkabe.
Fadar shugaban kasa ta zama abin dariya, ganin cewa tun ranar 27 Ga Agusta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya damka wa Shugaba Muhammadu Buhari binciken zargin harkallar kwangilar datse ciyawa ta Babachir Lawal, Sakataren Gwamnatin Tarayya, da harkallar milyoyin daloli ta Daraktan Hukumar tsaro, amma har yau Buhari bai bayyyana laifin su ko rashin laifin su ba.
Wasu da dama magoya bayan PDP na ganin cewa a yanzu ne daidai lokaci da ‘yan takara daga jam’iyyar Adawa, PDP ya kamata a ce sun fara daura warki su na rawa a cikin fagen siyasa, musamman yanzu da gwamnatin Buhari ke fama da rantse-rantsen neman wanda ya sa hannu a kwangilar naira bilyan 640 ta kamfanin NNPC.
To sai dai kuma ana ganin banda Sule Lamido, har yau babu wanda ya fito kuru-kuru ya nuna ya na bukata. Ko da ya ke dai akwai wasu da ke harbin iska a gefe su na neman ingiza shugaban jam’iyyar na yanzu, Ahmed Makarfi ya fito takara.
Ganin irin aikin da Sule ya yi wa al’ummar jihar Jigawa ne ya sa da dama ke ganin cewa babu kamar shi. Sannan kuma tunanin da wasu ke yi da wuya Buhari ya sake tsayawa takara, hakan zai kashe kaifin APC, domin da dama guguwar Buhariyya ce ta sa aka zabi jam’iyyar a 2015.
Dama kuma duk da irin hayagaga, ban-tsoro da firgita-karnai da aka yi wa PDP a 2015, da kuri’u miliyan 2 da kadan ta kayar da PDP.
Shin idan PDP ba ta fara motsawa tun yanzu ba, tsoron me ta ke ji ne? Ko har yanzu cikin shiri ta ke? Hausawa na cewa shirin zaune ya fi na tsaye. Wasu kuwa na cewa a’a, shirin tsayen ne dai ya fi na zaune.
To ko kalubalen da tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya yi ya shiga kunne masu neman kujerar shugaban kasa a karkashin PDP? Cewa ya yi PDP fa ba ta nuna jam’iyyar adawa ce. To ku me za ku ce?
Source: Premium Hausa
Title :
PDP Ta Shirya Kuwa?Ga Dama Amma Shiru
Description : Fitowar da Gwamnan jihar Ekiti ya yi, inda ya kada gangar neman takarar shugabancin kasar nan a 2019, karkashin jam’iyyar PDP ya tayar da k...
Rating :
5