Najeriya ta zama kasar Afirka ta farko daga cikin biyar da za su wakilci nahiyar a gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa da za a yi a shekara mai zuwa a Rasha.
Najeriyar ta samu wannan nasara ne bayan doke kasar Zambia da ci daya mai ban haushi, a wasan da suka buga jiya Asabar a Uyo babban jihar Akwa Ibom ta Najeriyar.
Tawagar ta Super Eagles ita ce ta daya a rukuni na biyu da maki 13 sai Zambia da maki bakwai sannan Kamaru mai maki shida da kuma Algeria da maki daya.
Kakakin majalisar wakilan Najeriya na cikin manyan jami'an da suka fara mika sakonsu na murna da wannan nasara.
Ya ce: "ina taya kungiyar Super Eagles murna sabili da nasarar da suka samu kan kasar Zambia, dalilin da yasa zasu wakilci kasarmu a gasar kwallon kafa na duniya a Rasha nan da watan Yunin 2018.
"Kungiyar ta Super Eagles ta yi rwar gani, kuma muna alfahari da ita. Kasancewa ita ce kasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta sami cancantar zuwa wannan gasar ba karamin kokari ne ba".
Sauran 'yan Najeriya daga sassan daban-daban na kasar suma sun nuna farin cikinsu a wata hira da suka yi da BBC daga birnin Kano.
Ibrahim Abba Tangalashe ya ce duka da cewa Najeriya ta sami nasara a wannan wasan, akwai sauran aiki a gaban kungiyar.
"Akwai 'yan wasa da ya kamata a canza su, kua kasar Zambia tafi buga wasa a wannan karawar ta Uyo," inji shi.
Shi kuwa Faisal Yusuf Maitaya cewa ya yi: " Najeriya tayi matukar kokari a wannan rukuni da ake kira 'Group of death', ta yadda ta lashe dukkan wasannin da ta buga illa daya".
Ga hotunan yadda ta kaya a filin wasan kwallo dake Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Source: BBC Hausa
Title :
Nigeria Zata Gasar Russia 2018
Description : Najeriya ta zama kasar Afirka ta farko daga cikin biyar da za su wakilci nahiyar a gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa da za a yi a sheka...
Rating :
5