Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi amincewar Majalisar dattawa domin karbo bashin dala biliyan 5.5.
A wata wasika da ya aikewa Majalisar, Shugaba Buhari ya ce daga ciki kudaden, za a yi amfani da dala biliyan 2.5 ne don sayen takardun lamuni daga kasashen Turai a kasuwannin duniya.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, wanda ya karanta wasikar a zauren Majalisar, ya ce za kuma za a yi amfani da takardun lamunin ne don aiwatar da wasu muhimman ayyuka a kasafin kudin shekarar 2017.
Ya kara da cewa sauran rancen da za a karbo za a yi amfani da su wajen biyan basussuka na cikin gida.
Muhimman ayyukan da za a aiwatar sun hada da aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila, da hanyar sauka da tashin jirage na biyu a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Akwai kuma ayyukan samar da layukan jiragen kasa da babbar hanyar Bonny da ke kudancin kasar, wadda ta hada da babbar gadar da ta ratsa kogin Opobo.
Source: BBC Hausa
Title :
Nigeria Taci Bashin Biliyan Daga Turai
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi amincewar Majalisar dattawa domin karbo bashin dala biliyan 5.5. A wata wasika da ya aikewa Maja...
Rating :
5