Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai.
Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka.
"Wannan ne ya sa gidauniyata ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can," kamar yadda ya ce.
Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.
"Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun 'yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin," in ji shi.
Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara a fadin kasar.
Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote - wanda dan kasar ne.
Kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi yawan samun mace-macen mata wajen haihuwa da kuma na kananan yara.
Source: BBC Hausa
Title :
Nigeria Nada Muhimmanci A Gurina-Bill gate
Description : Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai. Bill Gates...
Rating :
5