Najeriya ce ta farko da ta fara samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya daga nahiyar Afirka da ake sa ran kasashe biyar za su wakilceta a Rasha a 2018.
Najeriya ce ta jagoranci rukuni na biyu da maki 13, sai Zambia da maki bakwai sannan Kamaru da maki shida sai Algeria ta hudu da maki daya kacal.
Wannan ne karo na uku a jere da Super Eagles ke zuwa gasar cin kofin duniya, kuma na shida jumulla. Nigeria ta kai wasannin zagaye na biyu a gasar 1994 da 1998 da kuma 2014.
Ko mai ya kamata Nigeria ta yi domin ta taka rawar gani a wasannin da za a yi a Rasha.
Source: BBC Hausa