A Najeriya, wata kotu ta yanke wa mutum 20 hukuncin daurin shekara biyar zuwa shekara takwas a gidan yari bayan samun su da laifin zama 'yan kungiyar Boko Haram.
Wasu majiyoyi na shari'a sun shaida wa manema labarai cewa kotun da ke zama a asirce a wata cibiya ta sojoji da ke garin Kainji a jihar Neja ta kuma wanke fiye da mutum 80 saboda da rashin kwararran hujjoji da ke tabbatar da su 'yan Boko Haram ne.
Sai dai ba za a saki mutanen ba sai an yi masu wani shiri na raba su da tsattsauran ra'ayi da kuma gyara halayensu.
Ana saran kimanin mutum 7,000 da ake zargi za su fuskanci tuhume-tuhume a kotuna da ke zama a cibiyoyin tsare mutane daban-daban a fadin kasar.
Wannan shi ne shari'a mafi girma da ke da nasaba da ta'addanci a tarihin Najeriya.
Wadanda ake zargin sun kwashe shekaru ana tsare da su ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International dai ta nuna damu wa kan yadda ake yi wadanda ake zargi 'yan Boko Haram shari'a cikin sirri, tana mai cewa hakan zai hana yi wa wadanda ake zargin adalci.
Tun lokacin da aka fara tarzomar ta Boko Haram a arewacin Najeriya shekaru takwas da suka gabata, kimanin mutane 9 ne aka samu da laifi a kotu bisa alaka da kungiyar.
Source: BBC Hausa
Title :
Najeriya Ta Yanke Wa 'Yan Boko Haram 20 Hukunci
Description : A Najeriya, wata kotu ta yanke wa mutum 20 hukuncin daurin shekara biyar zuwa shekara takwas a gidan yari bayan samun su da laifin zama ...
Rating :
5