Gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta karrama Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta hanyar gina mutum-mutuminsa na tagulla tare da sanya wa wani titi sunansa.
Haka kuma an bai wa Mista Zuma wata sarautar gargajiya da kuma lambar yabo mafi girma a yankin, a yayin wata ziyara da ya kai jihar ta Imo a ranakun Asabar da Lahadi da ta wuce.
Sai dai hadakar kungiyar fararen hula naThe Civil Society Network Against Corruption, a kasar ta yi tur da wannan girmamawar.
Haka kuma hadakar da ke da kungiyoyi 150 a karkashinta ta yi Allah-wadai da gwamnan jihar, Rochas Okorocha saboda yadda ya nuna Mista Zuma a matsayin wani gwarzo ga "matasan Afirka" duk kuwa da cewa an kwashe shekaru kusan goma ana zarginsa da aikata cinhanci da rashawa.
Sanawar da ta fitar ta dora ayar tambaya kamar haka:
"Shin gwamna Okorocha bai san cewa mutanen Afirka ta Kudu na neman Zuma ya sauka daga shugabancin kasar ba ne a halin yanzu, saboda abin kunyar da ya janyo musu da kuma tozarta kasar Nelson Mandela?"
Karramawar dai ta zo ne 'yan kwanaki bayan kisan wata 'yar Najeriya, Jelili Omoyele, mai shekaru 35 a Afirka ta Kudu.
Masu amfani dandalin sada zumunta na Twitter da dama ne suka bayyana mamakinsu a kan batun kamar haka:
Yayin da muke murna da hukuncin da aka yanke a kan muryoyin da aka nada, muna fatan ganin Zuma ya sauka, sai gashi a Najeriya ana karrama shi.
With hundreds of counts of corruption charges against him, Jacob Zuma, somewhere in Nigeria 🇳🇬 stands as a deity. The gods must be crazy.
Jacob Zuma na fuskantar daruruwan zarge-zargen cin hanci da rashawa, sai gashi can a Najeriya, ana masa kallon wani abin girmamawa. Abincin wani gubar wani
Source: BBC Hausa
Title :
Mutum Mutumin Zuma:Okorocha Nashan Suka
Description : Gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta karrama Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta hanyar gina mutum-mutuminsa na tagulla t...
Rating :
5