Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce fiye da mutum miliyan 50 ne ke rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba a kasar.
Farfesa Osinbajo ya fadi hakan ne a wani taron kasashen Afirka da jaridar Financial Times ta shirya a London.
Sai dai mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatinsu tuni ta fara daukar matakan inganta tare da samar da wutar lantarkin, da suka hada da samar da lantarki ta hasken rana ga gidaje 20,000 a kauyuka daban-daban.
Farfesa Osinbajo ya ce: "Akwai damarmaki sosai a bangaren wutar lantarkinmu, musamman ma da muke kokarin inganta bangaren."
Matsalar wutar lantarki dai a Najeriya gagaruma ce da aka dade ana fama da ita, kuma tana yawan durkusar da al'umara musamman na kasuwanci da ci gaban masana'antu.
Ko a farkon shekarar nan ma kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya yi korafi a kan rashin isasshiyar wutar lantarki a kasar, inda ya ce, 'An kashe tirilyan uku a wutar lantarki a banza
Ya kuma kara da cewa wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa ba ta wuce karfin Megawatz 5000 ba tun fiye da shekara 50 da suka gabata.
Masu sharhi da dama na ganin tsare-tsaren gwamnatocin baya kan sha'anin wutar ne suka kasa yin tasiri.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutum Miliyan 50 Basuda Wutan Lantarki A Nigeria-Osinbajo
Description : Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce fiye da mutum miliyan 50 ne ke rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba a k...
Rating :
5