Ana ci gaba da aikin nemo mutane da daman da suka nutse a cikin wani kogi sakamakon hatsarin jirgin ruwan fasinja lokacin da suke kan hanyarsu cikin karamar hukumar Yawuri a jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga kauyen Jalbabu, inda ya nufi zuwa Yawuri dauke da fasinjojin da ake tsammanin adadinsu ya kai 50 zuwa 60.
Shugaban karamar hukumar Yawuri, Alh Musa Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, ya zuwa maryacen ranar Laraba an gano tare da yi wa gawawwakin mutum 15 jana'iza.
A cewarsa wasu daga cikin mutanen da ke cikin jirgin sun kubuta amma akwai wasu da dama wadanda har yanzu ba a iya gano su don haka ake ci gaba da bincike fasinjojin da ake kyautata tsammanin suna cikin ruwa.
Ya ce, jirgin ya yi hatsari ne sakamakon karo da wani kututture a tsakiyar kogi, lamarin da ya sa ya tsage sai kuma mutanen da ke ciki suka tsorata daga nan jirgin ya kife da su.
Ko a cikin watan jiya ma, wani hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 50 a cikin kogin Neja.
Musa Muhammad ya ce wasu daga cikin fasinjojin da ke jirgin, sun samu fitar da kansu, wasu kuwa sai da aka taimaka musu saboda ba su iya ninkaya ba.
Ana danganta aukuwar hatsarin jiragen ruwa da cunkoson da ake yi musu, ta hanyar daukar mutane da kaya fiye da kima da kuma rashin yashe kogunan da ake sufuri a cikinsu.
Shugaban karamar hukumar Yawurin, ya ce yanzu ana wayar da kan direbobi jiragen ruwa kai a yankinsa, game da muhimmancin bin ka'ida wajen daukar mutane, sannan su tabbatar da lafiyar jiragensu a kowanne lokaci.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutane Shabiyar Sun Halaka Sanadiyan Hatsarin Jirgin Ruwa A Jihar Kebbi
Description : Ana ci gaba da aikin nemo mutane da daman da suka nutse a cikin wani kogi sakamakon hatsarin jirgin ruwan fasinja lokacin da suke kan hanyar...
Rating :
5