Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan uku ne ke cikin hatsarin yunwa a lardin Kasai mai fama da rikici na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Shugaban shirin samar da abinci na Duniya, David Beasley, ya fada wa BBC cewa tuni kananan yara da dama suka riga mu gidan gaskiya saboda yunwa.
Ya kuma ce ana bukatar tallafi cikin gaggawa don kare karin wasu dubban daruruwan mutane daga mutuwa a watanni masu zuwa.
Rikici tsakanin dakarun gwamnati da abokan kawancensu a hannu guda kuma da sojojin sa-kai ne ya ta'azzara farin da ake fama da shi a yankin.
Ana zargin duka bangarorin biyu da far wa fararen hula.
Source: BBC Hausa
Title :
Mutane Na Mutuwa Sabida Yunwa A Congo
Description : Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan uku ne ke cikin hatsarin yunwa a lardin Kasai mai fama da rikici na Jamhuriyar Dimokradi...
Rating :
5