Gwamnatin tarayya ta sami tabbacin bullowar cutar ‘Monkey Pox’ inda uku cikin jinin mutane 31 din da aka gwada na dauke da cutar.
Gwamantin Najeriya ta sami tabbacin hakan ne bayan ta kai jinin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar gwaji a kasar Senegal.
Yayin da yake sanar da hakan a yau Litini ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga mutanen kasar nan da su kwantar da hankalin su musamman game da cutar domin ‘Monkey Pox’ din iri biyu ne da na tsakiyar Afrika da na yammacin Afrika.
‘‘Ina mai tabbatar muku da cewa cutar ‘Monkey Pox’ na yammacin Africa baya illatar da mutane kamar na tsakiyar Afrika’’.
Source: Premium Hausa
Title :
Mutane 3 Ne Kacal Cikin 31 Ke Dauke Da Cutar Money Pox
Description : Gwamnatin tarayya ta sami tabbacin bullowar cutar ‘Monkey Pox’ inda uku cikin jinin mutane 31 din da aka gwada na dauke da cutar. Gwamantin...
Rating :
5