Shugaban kula da harka da jama’a na hukumar bada agaji na jihar Neja NSEMA Hussaini Ibrahim ya sanar da mutuwan mutane 22 sanadiyyar kifewar jirgin ruwa a Mahuta dake karamar hukumar Agwara a jihar.
Ya sanar da haka ne da yake zantawa da manema labarai a garin Minna.
Ya ce jirgin ruwan ta kife ne yayin da mutanen ke hanyar zuwa Mahuta daga Yauri jihar Kebbi.
” Mutanen sun sami labarin cewa an GA wani duste dauke da rubutun Arabi a Mahuta wanda hakan ne sanadiyyar ajalinsu.”
Ya ce an tsamo mutane bakwai daga cikinsu da ransu inda suka ce jirgin ruwan ya kife ne sanadiyyar karon da ta yi da wata katako a cikin ruwan.
Ya ce an kai gawawwakin mutanen da suka rasu Damon ajiye gawa na wani asibiti da ke Yauri.
Source: Premium Hausa