Wani mai kama macizai a Najeriya ya ce dabara suke amfani da ita wajen kama maciji amma ba dogaro da jikon magani ba.
Malam Ali Garba wanda a yayin zantawa da wakilinmu Ishaq Khalid yake tare da macizai kimanin bakwai da ya kamo ciki har da kububuwa da gamsheka da kasa ya ce ya fara sana'ar kama macizai ne tun shekarar 1999 don ceton rayukan jama'a.
Akasarai dai sai an kamo macijin da ya yi sara kafin a san kowanne iri ne, idan za a yi wa mutum magani.
A cewar Ali Garba ana amfani da basira ne wajen kama maciji. Kuma sukan kamo su da yawa, su kai asibitin Kaltungo a jihar Gombe.
"Za ka ga an kawo mutum ba yadda yake, to kuma idan ba an kamo macijin ba, ba za a samu asalin maganin macijin ba, ko kuma yadda za a cire dafinsa a yi maganin ba," in ji shi.
Ya kara da cewa sukan shiga daji su kamo su, idan suka kamo su kuma sai a tara macizan kafin a kai su inda za a cire dafin.
Shi ma wani mai kama macijin Dala Usaini ya ce sun sani cewa sana'arsu tana cike da hatsari, don kuwa "da ya sare ka a wurin, idan babu mai taimakonka to ka gamu da nakasa".
"In ba mutum a kusa da kai kafin ka dawo gida, in ba Allah yai maka nisan kwana ba, za ka bar duniya a take," in ji shi.
Ya ce suna neman taimako don tsare jiki, sai dai duk da haka macijin ya taba saransa.
Dala Usaini ya ce maciji kan sare su amma saboda sun sha magani, abin ba ya nakasa su kamar wanda bai taba amfani da magani ba.
Shi ma Ali Garba ya ce maciji ya sare shi lokacin da ya je kamo shi, don ya kai a yi magani, inda ya yi ta zuba masa dafi a hannu.
"Lokacin da ake neman maciji, ba magani a nan (asibitin Kaltungo) ni kuma aka nemi a kamo macijin don a yi magani.
Na sa hannu na kamo shi, sai ya sa hakori kuma maimakon ya sa dafi kadan amma sai ya yi ta zubawa kafin na bude akwati na sa shi wurin ya riga ya zama baki. Na ji kamar an dora min dutse a kai."
Ali Garba ya ce daga baya sai da aka yanke yatsan don gudun kada ya shafi hannun gaba daya kuma dole a yanke shi.
Ya koka kan yadda mutane kan tsaya amfani da magungunan gargajiya a gida bayan maciji ya sari mutum har sai dafin ya ratsa jiki, abin da ke da matukar hatsari.
"Gaskiya akwai magani amma akwai wasu masu yaudarar mutane a kan magani, za ka ga wasu suna tallan maciji...amma yawanci suna cire hakoran ne su zo suna wannan abu a kasuwa."
Dala Usaini ya ce a yankin Gombe sun fi kama kububuwa, wanda kuma hatsabibin macijin ne da ba ya tsoron mutum.
Source: BBC Hausa
Title :
Muna Kama Macizai Ne Don Ceton Rayukan Jama'a
Description : Wani mai kama macizai a Najeriya ya ce dabara suke amfani da ita wajen kama maciji amma ba dogaro da jikon magani ba. Malam Ali Garba wanda...
Rating :
5