Ministan lafiya na kasar Tunisiya ya rasu sakamakon bugun zuciya bayan ya shiga wani gangamin gudun sassarfa don tallafa wa yaki da cutar daji.
Slim Chaker, mai shekara 56, ya kamu da rashin lafiya bayan ya yi gudun da ya kai nisan mita 500, daga bisani kuma ya mutu a wani asibitin soja, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar.
Fira ministan Tunisiya Youssef Chahed ya ce ya yi rashin "dan'uwa kuma abokin aiki", wanda ya mutu a kan wani managarcin aikin jin kai.
An gudanar tseren yada kanin wanin ne a garin Nabeul na gabar teku ranar Lahadi don tara gudunmawar da za a gina wani karamin asibitin kula da kananan yara da ke fama da cutar daji.
A cikin watan jiya ne aka nada Mista Chaker ministan lafiya bayan wani gagarumin garambawul da aka yi wa majalisar ministocin Tunisiya.
Shi dai tsohon ma'aikacin banki ne wanda ya yi aiki a ma'aikatar kudi da ta wasanni da matasa bayan hambaras da gwamnatin shugaba Zine al-Abidine Ben Ali a shekara ta 2011.
Alamomin bugun zuciya
Ciwon kirji - jin karta, takura ko matsi a tsakiyar kirji
Ciwo a sauran gabobin jiki - Ana iya jin kamar ciwon yana yawo daga kirji zuwa hannuwa (galibi hannun hagu amma dai ana iya jin ciwon a duk hannuwa), da muka-muki da wuya da baya da mara.
Jiri
Yawan gumi
Numfashi sama-sama
Tasowar haraswa ko kuma haraswar
Shiga cikin damuwa
Tari da huci
Ko da yake, ciwon kirjin a akasarin lokuta kan zo da tsanani, wasu mutane ka iya jin ciwon kadan irin na kullewar ciki. A wasu lokuta, ba ma za a ji ciwon kirjin ba, musammam ma mata, tsofaffi da mutane masu ciwon suga.
Majiya: Hukumar Lafiya Ta Ingila
Source: BBC Hausa
Title :
Ministan Lafiya Ya Mutu Bayan Ya Shara Gudu
Description : Ministan lafiya na kasar Tunisiya ya rasu sakamakon bugun zuciya bayan ya shiga wani gangamin gudun sassarfa don tallafa wa yaki da cutar da...
Rating :
5