A wannan makon a filin Adikon Zamani, muna nazari ne kan jinin al'adar mata. Duk da cewar wannan abu ne wanda ko wacce mace ke yi, jama'a har da matan kansu ba sa son tattauna batun.
A wasu wuraren ana yi wa jinin al'ada kallon wani abu mara kyau, mai ban kunya.
Saboda haka sai mata su buya lokacin jinin domin guje wa ba'a da kunyatarwa.
A shirinmu na wannan makon mun tattauna dalilin da ya sa wasu ke ganin jinin al'ada tamkar abin kunya ne a arewacin Najeriya.
Mun kuma tattauna hanyar da ta fi dacewa a bi wajen kasancewa cikin tsafta a wannan lokacin da ke cike da damuwa da matsaloli a rayuwar ko wacce mace.
Wasu suna fuskantar ciwon jiki da ciwon mara da warin jiki da yawan sauya halayya da son abubuwa daban-daban da dai sauransu.
Tsanani da kuma yawan aukuwar irin wadannan matsalolin sun bambanta daga mace zuwa mace.
Dokta Yelwa Usman ta halarci shirin domin tabbatar mana da cewar jinin al'ada wani jini ne da yake fitowa daga jikin mace wanda Ubangiji Ya tsara halittarta a kan haka.
Kuma rashin tsabtace jiki yadda ya kamata da rashin kula na iya haifar da matsalar da za ta hana mace haihuwa.
Amfani da tsumma a ko wanne wata na da hatsari sosai domin tsumokara na kwashe kwayoyin cuta wadanda za su iya jirkita yanayin al'aura.
Hakan na iya sa mace ta kamu da cututtuka. Abin da ya fi, in ji likitoci, shi ne amfani da audugar tare jini, a kuma dinga sauyata duk bayan sa'a shida.
Wanne alamu ku ke gani a lokacin jinin al'adarku? Wadanne kalubale ku ke fuskanta? Kuna iya aiko mana da ra'ayoyinku da sakonninku a shafinmu na Facebook.
Source: BBC Hausa
Title :
Meyasa Mata Ke Kunyar Tattauna Batun Jinin Al'ada?
Description : A wannan makon a filin Adikon Zamani, muna nazari ne kan jinin al'adar mata. Duk da cewar wannan abu ne wanda ko wacce mace ke yi, jama...
Rating :
5