Batun al'adar da mata ke yi na jinin haila duk wata, wani al'amari da ba a faye tattaunawa a kansa ba, musamman a kasashen da ke girmama al'adu kamar Najeriya.
Hakan ce ta sa mata ke shiga wani yanayi na rashin sanin ainihin abin da ya kamata su yi ta fuskar kula da kansu don gudun kamuwa da wasu cututtuka a sakamakon rashin tsafta.
Wasu alkaluma da kungiyar WaterAid mai fafutukar ganin an samar da tsaftataccen ruwan sha da yanayi mai tsafta a rayuwar bil-Adama ta fitar a watan Mayun bana, sun nuna cewa a kullum mata kusan miliyan dari takwas ne ke al'ada; sai dai galibinsu sukan rika boye-boye da kuma fuskanci muzgunawa a wannan lokaci.
A cewar kungiyar an yi watsi da bukatun mata da 'yan mata game da al'ada, lamarin da ke haifar da asara iri-iri ga al'umma, kama daga asarar damar zuwa makaranta zuwa ga ta tattalin arziki.
Shin wadanne bukatu mata ke da su a lokacin al'ada?
Me ya kamata su yi? Wanne taimako ya kamata al'umma ta ba su?
Kungiyar ta ce mace daya cikin mata uku a ko ina a fadin duniya ba sa samun damar amfani da tsaftataccen ban daki a yayin da suke al'ada, wanda hakan yana nufin zai yi matukar wahala su samu walwala a lokacin da suke al'adar.
Da yawan mata musamman wadanda ke zaune a karkara ko wadanda ba su da hali sosai na amfani da kyalle ko tsumma a yayin da suke al'ada.
Sai dai wani bincike ya gano cewa, amfani da tsumma ko kyalle da mata ke yi wajen yin kunzugu a lokacin da suke jinin al'ada, na janyo kamuwa da cutuka da dama.
Dokta Yalwa likitar mata ce a asibitin Maitama da ke birnin Abuja, ta shaida wa BBC cewa, daga cikin cutukan da ake kamuwa da su sakamakon amfani da tsumma musamman marar tsafta a matsayin kunzugu, akwai kuraje da kaikayi, wani lokacin ma har da fitar da ruwa mai wari daga al'aurar mata.
Hyeladzira Shalangwa, jami'a a kungiyar WaterAid ta ce duk da cewa dalilai na rashin sukuni ke sa mata amfani da kyalle ko tsumma maimakon audugar mata ta zamani, hakan ba zai zama dalilin da zai hana su tsaftace shi ba ta hanyoyin da suka dace don magance kamuwa da cututtuka.
Dokta Yalwa ta ce: "Yana da kyau matan da ke amfani da kyalle su dinga sauya shi kamar sau uku a rana, su kuma dinga wanke shi da ruwan zafi da gishiri a kuma goge shi ko da da dutsen dugar gargajiya ne na gawayi, domin hakan zai taimaka wajen kashe kwayoyin cutar da suke kai."
Mutane da dama dai na ganin tun da ba za a iya shawo kan wannan matsala ba saboda ganin cewa tana da alaka da wadatar mutum, to yana da kyau masana a harkar lafiya su dinga wayar da kai da ba da shawarwari ga mata kan yadda za su dinga tsaftace kyallayen da suke amfani da su.
Source: BBC Hausa
Title :
Meyasa Mata Ke Amfani Da Tsumma Yayin Jinin Al'ada
Description : Batun al'adar da mata ke yi na jinin haila duk wata, wani al'amari da ba a faye tattaunawa a kansa ba, musamman a kasashen da ke gir...
Rating :
5