A jerin wasikunmu da suka fito daga 'yan jaridun Afirka, Editan jaridar Daily Trust ta Najeriya, Mannir Dan Ali, ya yi duba ne game da dalilin da ya sa kasar da take da yawan al'umma wato Najeriya har yanzu ta gaza bai wa yaran kasar ingantaccen ilimi.
Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Nasir el-Rufai, mutum ne da ake ganin a matsayin mai yawan kawo batu mai cike da ce-ce-ku-ce.
A lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya kwanan nan, ya bayyana cewa sakamakon jarabawar da aka yi wa malaman firamare na jihar ya yi matukar ba da mamaki da takaici.
An yi musu jarabawar 'yan aji hudu ta 'yan shekara 10.
Kuma sai malaman sun ci a kalla kashi 75 cikin 100, in ji gwamnan.
Ya kara da cewa, "Amma abin bakin-cikin shi ne yadda kashi 66 bisa 100 na malaman suka fadi jarabawar warwas."
Ya yi zargin an bai wa malaman da ba su cancanta ba aiki, kuma ya yi alkawarin kawo karshen matsalar.
Sai dai sakataren kungiyar gwamnatin jihar Adamu Ango, ya musanta ikirarin gwamnan, ya kuma ce duk farfagandar kafafen yada labarai ce kawai.
Abin mamakin shi ne yadda malaman jihar suka nuna rashin jin dadinsu kan lamarin, musamman ma jarrabawar da aka yi musu a jere, inda suka ce wannan ne karo na uku da aka yi musu jarrabawar a bana.
Malaman sun ce da kamata ya yi a bayyana sakamakon sauran jarrabawar da suka yi in dai har gwamnan zai yi adalci.
Sun kuma ce har yanzu gwamnan bai biya su alawus-alawus din su ba na tsawon shekara biyu ba?
Har ila yau akwai matsalar ajujuwan karatu.
Wata rana wani abokina malamain makaranta ya gayyaceni mkarantar da yake koyar wa inda na ga ko wanne aji dauke da kusan dalibai 90 zuwa sama da 120.
Ko da yake yawancin malaman na shan fama wajen tafiyar da wadanann ajujuwa, inda yawancin yaran ma sun fi son zama a kasa, wasu suna wasa ko wannan ya tsokani wannan yadda karatun ma ba zai yiyu ba.
Shugabanni sun fi mayar a hankali wajen bayar da kwangilar gina ajujuwa da za a rika hango su daga waje, fiye da horar da su da kuma zaburar da su a kan aikinsu.
"Cibiyoyin da ake biyan kudi a ci jarrabawa"
Makarantu da dama sun fi mayar da hankali kan dalibai su samu sakamako mai kyau, amma a zahiri ba su san komai ba.
Har ila yau hakan ya sake kawo karuwar abin da ake kira "cibiyoyin da ake biyan kudi a ci jarabawa". Duk wanda ya je irin wadannan makarantu ko cibiyoyi yana da tabbacin samun kyakkyawan sakamako idan ya biya kudi.
Wani da yake koyarwa a makarantar gwamnati ya shaida min cewa, yana alfahari da irin wannan makarantu, domin ya ga dalibai da dama da suka shafe shekara 12 a makaranta, amma ba za su iya kwafar amsar tambayoyin da malamai suka rubuta musu a kan allo ba.
Wannan ya nuna dalilin da ya sa ba ya ga jarrabawar da ake yi ta kasa, jami'o'i da sauran kwalejin ilimi ke shirya wata jarrabawar ta musamman kafin su dauki dalibai.
Irin wadannan manyan makarantu sun tsaya kai da fata a kan sai sun sake shirya jarabawa ta kashin kansu don tabbatar da makin da ko wanne dalibi ya samu ba na bogi ba ne.
Daukar aiki ya zama abin takaici a wurin masu daukar ma'aikata wadanda suke cin karo da daliban da suka hada digiri amma da wuya su iya hada kwararan jumloli biyar.
Irin wadannan matsalolin da ake fuskanta a makarantu musamman na gwamnati ne yasa iyaye suka gwammace su zuba kudinsu su kai 'yayansu makarantu masu zaman kansu.
Dadin-dadawa kuma, 'yan Najeriya na tunkaho da makarantun da 'ya'yansu suke zuwa.
Amma sakamakon yawan yajin aikin da jami'o'i suke yi ya sa dalibai ba su da tabbas na lokacin kammala karatunsu, duk da cewa tun da fari an tsara lokacin kammala karatun.
Wannan yana matukar tayawar wa dalibai hankali musamman wadanda ba su da halin zuwa kasashen ketare yin karatu.
Wadanda ba za su iya biyan kudin karatu da sauran kudaden da ake kashewa a Amurka ba, ko kasashen Turai ko Asiya suna zuwa kasashen da ke makwabtaka da su, kamar su Jamhuriyar Benin da Ghana da Uganda da sauran kasashen Afirka.
A takaice dai 'yan Najeriya na dokin kashe kudinsu a wasu daga cikin jami'o'i masu zaman kansu a Ghana, da Benin da Nijar don samun damar yin karatu a can.
Sai dai kadan daga cikin 'yan Najeriyar ne suke iya biyan kudin makarantu masu zaman kansu da jami'o'i.
Duka dai, yawancin 'yan Najeriyar sun amince cewa akwai kalubale da dama da ake fuskanta a bangaren ilimi, ko da yake babu wata yarjejeniya da aka cimma a kan dalilin hakan da kuma hanyar da za a bi a magance matsalar.
Kalaman da gwamnan Kaduna ya yi za su iya jan hankali, sai dai ba lallai ne hakan ya inganta kwazon malaman ba.
Source: BBC Hausa