A jerin masu wasan motsa jiki da aka fi biya, mace daya ce take cikinsu - wato shahararriyar 'yar kwallan tennis Serena Williams.
Serena tana mataki na 51 kuma kudin da take samu ya gaza na Cristiano Ronaldo, dan wasan da ya fi samun kudi a duniya a cewar mujallar Forbes.
Tawagar mata 'yan kwallon kafa ta kasar Amurka ta samu kyautar dala miliyan biyu bayan ta ci gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2015.
Har ila yau, gasar kwallon kafa ta duniya ta maza kuma ta samar wa wadanda suka lashe kyautar dala miliyan 35 a shekarar 2014.
Wadannan 'yan misalai ne kawai da ke nuna gagarumin gibin biya a duniyar wasanni da ya dade da zama al'ada.
Sai dai kuma, bincike na baya-bayan nan, ya nuna cewa bambanci wajen samun kudin shiga tsakanin 'yan wasa mata da 'yan wasa maza ya ragu sosai a 'yan shekaraun da suka wuce.
Jumullar kashi 83 cikin 100 na wasanni a duniya yanzu suna biyan maza da mata kudi bai daya, in ji wani bincike kan fannoni 68 da sashen wasanni na BBC ya wallafa a watan Yunin da ya gabata.
Kudin da ake biyan mata yana karuwa ne tun shekara uku da suka wuce, kuma 35 daga cikin wasanni 44 da suka bayar da kyautar kudi suna biya bai daya ne.
Wannan ya yi kama da labari mai kyau, musammann idan aka kwatanata da shekarun da suka gabata - a shekarar 2014 kashi 70 cikin 100 na wasanni ne kawai suka samu suka cike gibin kudin biya,
Kuma a shekarar 1973 babu wani wasan da ya biya maza da mata bai daya.
"Mata sun fi fitowa a wasanni yanzu fiye da ko wane lokaci a tarihi," in ji wata sanar daga Hukumar Kula da mata ta Majalisar Dinkin Duniya.
Duk da haka sauyi na tafiyar hawainiya ta yadda za a dauki dogon lokaci kafin a kai ga samun biya bai daya a mataki na sama, in ji masana.
"Muna samun ci gaba, amman yana faruwa ne kamar tafiyar hawainiya," in ji Fiona Hathorn, darakatar kungiyar Women on Boards da ke fafatukar ganin mata suna shugabanci.
"Har yanzu duniyar wasanni ta kasance cike da maza a kan mata, kuma bambanci tsakanin maza da mata a wasu wasanni na da tayar da hankali sosai."
Kriket da Golf da kuma kwallon kafa suna cikin wadanda suka fi sabawa biya bai daya tare da snuka da sauransu.
Kasuwancin wasanni na duniya - da ya kai dala biliyan 145.3 , in ji kiyasin PwC- bai kai ga samar da daidaito tsakanin jinsin maza da mata ba.
"Ba zan iya tunanin wani fannin da yake da irin wannan gibin ba. Ya danganci irin halin da ake ciki a kasa da kuma wasa, na miji ka iya zaman biloniya kuma mace (wadda take irin wasan) ba za ta iya samun albashi mafi karanci ba," in ji Beatrice Frey, manajar hadin gwiwa na wasanni a hukumar da ke kula da mata ta Majalisa Dinkin Duniya.
Wadanda suka fi laifi
Bambance-bambance suna fitowa karara a wane mataki na harkar kwallon kafa mai biloyoyin kudade.
Wani bincike na kwanan nan da kungiyar Women on Boards ta fitar ya nuna cewa maza masu taka leda sukan samun abin da ya rubanya na mata sau hudu duk da cewa matan sun fi su kokari.
Gibin zai kara girma idan aka yi la'akari da jumullar kudin da aka biya.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ce take yanke iya kyautar da za a bayar a dukkan gasa biyun.
Ita ce ta ba da dala miliyan 15 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta duniya ta mata, kuma ta ba da dala miliyana 576 ga wadanda suka lashe gasar kwallon kafa ta maza.
Kuma a daidai lokacin da kyaftin din Ingila, Wayne Rooney, yake samun kudi dala 400,000 a ko wane mako, albashin takwararsa mace, Steph Houghton, bai taka kara ya karya ba idan aka yi la'akari da nashi - kimanin dala 1,600 a ko wane mako, in ji kafar Ladbrokes Sports.
Ana iya ganin irin wadannan gibin biya a wasu wasannin.
A wasan Golf, maza a gasar US Open suna neman samun kyuatar kusan dala miliyan $1.5 ne, kudin da ya rubanya kyautar da mata za su samu a gasar.
Ka dubi labarin Lydia Ko, daga kasar New Zealand, wadda ta zama mai karamar shekaru irin nata cikin ko wane jinsi da ta fara zama cikakkiyar 'yar wasan Golf a shekarar 2015.
A wanna shekarar ta samu kudin da ya gaza na dan wasan golf da ke matsayi na 25 a jerin sunayen gwanaye cikin maza na gasar PGA Tour, kamar yadda Newsweek ta bayyana.
Har ila yau, a gasar Kriket wata tawagar maza da ta lashe gasar cin kofin duniya za ta iya rubanya abin da mata za su samu fiye da sau bakwai.
Kuma ana maimaita gibin albashin a gasar kwallon kwando ta maza da ta mata da ta fi daraja duniya - NBA da WNBA.
"'Yar wasan da ta fi samun kudi a gasar kwallon kwando ta WNBA tana samun kashi daya cikin biyar na abin da dan wasan kwallon kwandon da yake karbar kudi mafi karanci a gasar maza NBA," in ji mujallar NBA .
'Kulob din yara'
Domin a samu daidaito, masana sun ce, bayar da kyaututtuka ba tare da la'akari da jinsi ba bai zai isa ba wajen kawar da matsalar sai an hada da daukar nauyi da talla da kuma sharuddan yarjejeniya.
Alal misali a fagen tennis, muhimman gasar da ake yi a ko wace shekara sun kaddamar da biya bai daya ga mata da maza tun shekarar 2007, duk da haka fitattun 'yan wasa maza sun fi mata samun kudi a ko wace shekara domin yarjejeniyoyi na daukar nauyi domin talla.
Shi ya sa Serena Williams ta kasance ita kadai a jerin sunayen 'yan wasa 100 da suka fi kudi ta mujallar Forbes.
"'Jerin 'yan wasa 100 da ke kan gaba ya fi zama na maza fiye da yadda aka saba", in ji wakilin mujallar Forbes kan wasanni Kurt Badenhausen a lokacin da aka fitar jerin sunayena watan Yuni.
"Maria Sharapova ta kasa shiga cikin jerin sunayen bayan an rage kudaden yarjejeniyoyin tallan da take da su."
Ronaldo ya samu dala miliyan 58 na alabashi da kyaututa, amman ya kara da dala miliyan 35m daga masu talla da masu daukar nauyi domin talla da kuma kudaden fitowa.
Ga kuma dan wasan golf Tigers Woods da kuma tauraron wasan tsere Usain Bolt, daukar nauyi domin talla ya kai kashi 90 cikin 100 na kudaden shigansu.
"Nuna wariyar jinsi ya zama ruwan dare gama duniya a fagen wasanni," in ji Frey.
"A matakin farko zai iya kasancewa domin mata ba sa iya wasannin da a al'adance ba na mata ba ne, lamarin da yake janyo wariya a tun suna kanana wanda zai bi su har zuwa lokacin da suka zama matasa zuwa gwanayen wasa."
Sannan, ta ce, yana nufin za a samu rashin daidaito a damarmaki a daukar nauyi da talla, har ya kai ga yawancin 'yan wasa mata a fadin duniya ba sa iya ciyar da kansu daga sana'o'insu na wasanni.
Kuma yanayin na ta ci gaba.
"Ga mata 'yan wasa da suka yi murabus lamarin na tare da matsaloli. Bawai ba su samu kudi mai yawa ba ne kawai,ta yiwu ba su fansho ko gida ko kuma tsaro ba," in ji Hathorn.
"Kuma wannan wata matsala ce ga burin 'yan mata: me ya sa za su so zama 'yan wasa in har haka makomarsu za ta kasance?"
Source: BBC Hausa